@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Wata rana Imam Sadiq (A. S) suna zaune da Alqamata suna tattaunawa, bayan sunyi wasu maganganu sai Imam (A. S) yake ce masa;
قَالَ الصَّادِقُ ع يَا عَلْقَمَةُ مَا أَعْجَبَ أَقَاوِيلَ النَّاسِ فِي عَلِيٍّ ع كَمْ بَيْنَ مَنْ يَقُولُ إِنَّهُ رَبٌّ مَعْبُودٌ وَ بَيْنَ مَنْ يَقُولُ إِنَّهُ عَبْدٌ عَاصٍ لِلْمَعْبُودِ وَ لَقَدْ كَانَ قَوْلُ مَنْ يَنْسُبُهُ إِلَى الْعِصْيَانِ أَهْوَنَ عَلَيْهِ مِنْ قَوْلِ مَنْ يَنْسُبُهُ إِلَى الرُّبُوبِيَّةِ يَا عَلْقَمَةُ أَ لَمْ يَقُولُوا فِي اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ إِنَّهُ ثَالِثُ ثَلَاثَةٍ أَ لَمْ يُشَبِّهُوهُ بِخَلْقِهِ أَ لَمْ يَقُولُوا إِنَّهُ الدَّهْرُ أَ لَمْ يَقُولُوا إِنَّهُ الْفَلَكُ أَ لَمْ يَقُولُوا إِنَّهُ جِسْمٌ أَ لَمْ يَقُولُوا إِنَّهُ صُورَةٌ تَعَالَى اللَّهُ عَنْ ذَلِكَ عُلُوّاً كَبِيراً يَا عَلْقَمَةُ إِنَّ الْأَلْسِنَةَ الَّتِي يَتَنَاوَلُ ذَاتَ اللَّهِ تَعَالَى ذِكْرُهُ بِمَا لَا يَلِيقُ بِذَاتِهِ كَيْفَ تُحْبَسُ عَنْ تَنَاوُلِكُمْ بِمَا تَكْرَهُونَهُ فَ اسْتَعِينُوا بِاللَّهِ وَ اصْبِرُوا إِنَّ الْأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُها مَنْ يَشاءُ مِنْ عِبادِهِ وَ الْعاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ فَإِنَّ بَنِي إِسْرَائِيلَ قَالُوا لِمُوسَى أُوذِينا مِنْ قَبْلِ أَنْ تَأْتِيَنا وَ مِنْ بَعْدِ ما جِئْتَنا فَقَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ قُلْ لَهُمْ يَا مُوسَى عَسى رَبُّكُمْ أَنْ يُهْلِكَ عَدُوَّكُمْ وَ يَسْتَخْلِفَكُمْ فِي الْأَرْضِ فَيَنْظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ[9].
FASSARA
" Yaa Alqamata, bana mamakin maganganun mutane game da Ali (A. S), sau nawa wasu ke cewa shi Ubangiji ne abin bautawa? Wasu kuma suna cewa shi bawa ne (amma) mai sabawa (Allah) ?
Tabbas, maganganun masu nasabta shi da aikata sabo yafi muni (abin qyama) gare shi fiye da masu nasabta shi ta kalmomi na rububiyya.
Yaa Alqamata! Ashe basu fada ba game da Allah cewa shi dayan uku bane (Thaalithus-thalaatha) ?
Ashe basu siffanta Shi da halittunsa ba?
Ashe basu ce Shi zamani bane (mai cancanzawa) ?
Ashe basu ce Shi falaki bane?
Ashe basu ce Shi jiki bane?
Ashe basu ce Shi hoto bane?
Allah ya daukaka daga haka daukaka mai girma !
Yaa Alqamata ! Lalle harsunan dake jijjuya zatin Allah suna ambatonSa da abinda ba ya riskuwa ga zatinSa , to, ta yaya kuwa za su katangu daga jijjuya ku da abinda kuke qinsa ?
" KU NEMI TAIMAKON ALLAH KUMA KUYI HAQURI , LALLE QASA TA ALLAH CE YANA GADAR DA ITA GA WANDA YASO DAGA BAYINSA , KUMA KYAKKYAWAN QARSHE NA GA MASU TSORON ALLAH ."
Haqiqa Banu Isra'ila sun cewa Musa (A. S);
" Sun cutar damu gabanin (kazo mana) da kuma bayan (ka zo mana) ."
Sai Allah (T) ya cewa Musa (A. S) ka fada musu cewa;
" AKWAI TSAMMANIN UBANGIJINKU YA HALAKAR DA MAQIYANKU KUMA YA SHUGABANTAR DA KU CIKIN QASA, SANNAN YAYI DUBI YAGA YA ZA KU AIKATA. "
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج67، ص: 4
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
28th Sep, 2020/ 11th Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com