Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Jinjinawa Sojan Saman Kasar

Ayatullah Sayyid Imam Khamnei wanda ya fitar da sako a yau Litinin ya jinjinawa kokarin da dakarun sama na Iran suke yi wajen kare kasa.
Birgediya Janar Muhammad Shrazi wanda shi ne shugaban bangaren soja na ofishin jagoran juyin ne ya karanta sakon ta hanyar tattauanwa ta wayar tarho da Birgediya janar Alireza Sabahifard da shi ne kwamandan sojan sama na Iran.

Wani sashe na sakon jagoran ya kunshi cewa; Kasar Iran tana samun tsaronta ne daga zama cikin shirin da sojojin sama da kuma sa idon da suke yi.

Har ila yau Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kara da cewa; “Mutanenmu na kwarai suna jinjinawa kwazo da kokarin da suke yi dare da rana.”

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post