Isra’ila Ta Sake Kai Jerin Hare haren Sama A Siriya

Majiyoyin tsaro a Siriya, sun ce makamman garkuwa daga hare haren sama na kasar, sun sake dakile wasu jerin hare haren Isra’ila a cikin daren jiya Litini.

Wannan dai shi ne hari na biyu da Isr’aila ta kai kan kasar ta Siriya, a cikin watan Agusta da mukayi ban kwana da shi.

Kamfanin dilancin labaren Siriya na SANA, ya ce makiya sun kai hare hare a yankunan kudancin kasar, kuma hare haren sun yi ajalin mutane biyu da kuma jikkata wasu bakwai.

Saidai wasu bayanai da kungiyar dake sanya ido kan lamuran kare hakkin dan adam ta OSDH, ta ce mutane 11 ne da suka hada da sojojin gwamnatin Siriya 3 da mayakan sa kai 7 da kuma farar hula guda suka rasa rayukansu a harin.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post