Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Mahamadu Isufu, inda suka tattauna kan batutuwa da dama.
Yayin tattaunawar data wakana da yammacin jiya Litini, shugaba Rauhani, ya ce kasarsa a shirye ta ke ta karfafa hulda da kasar ta Nijar, ciki harda yaki da ta’addanci, baya ga wasu bangarori da suke da alaka a tsakaninsu.
Shugaba Ruhanin, ya kuma godewa kasar ta Nijar, akan goyan bayan data bai wa Iran, yayin kada kuri’ar kin amincewa da daftarin dokar Amurka, na neman tsawaita takunkumi hana sayen makamai ga kasar ta Iran, kamar yadda fadar shugaban kasar Iran ta wallafa a shafinta na intanet.
Kasashen Iran, da Nijar dai na da kyakyawar alakar diflomatsiyya ta kusan shekaru 40.
SOURCE: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Tags:
Labaran Duniya