Ilimi Yafi Dukiya Da Abubuwa Bakwai !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Da shike duniya aka fi so da kuma fifitata kan komai sai ya zamana cewa an fi ganin darajar mai dukiya ko mai mulki akan mai ilimi , alhali ilimi ne mafifici kan dukiya. 


Karanta wannan riwayar daga Imam Ali (A. S). 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


108 وَ عَنْهُ ع أَيْضاً الْعِلْمُ أَفْضَلُ مِنَ الْمَالِ بِسَبْعَةٍ الْأَوَّلُ أَنَّهُ مِيرَاثُ الْأَنْبِيَاءِ وَ الْمَالَ مِيرَاثُ الْفَرَاعِنَةِ الثَّانِي الْعِلْمُ لَا يَنْقُصُ بِالنَّفَقَةِ وَ الْمَالُ يَنْقُصُ بِهَا الثَّالِثُ يَحْتَاجُ الْمَالُ إِلَى الْحَافِظِ وَ الْعِلْمُ يَحْفَظُ صَاحِبَهُ الرَّابِعُ الْعِلْمُ يَدْخُلُ فِي الْكَفَنِ وَ يَبْقَى الْمَالُ الْخَامِسُ الْمَالُ يَحْصُلُ لِلْمُؤْمِنِ وَ الْكَافِرِ وَ الْعِلْمُ لَا يَحْصُلُ إِلَّا لِلْمُؤْمِنِ خَاصَّةً السَّادِسُ جَمِيعُ النَّاسِ يَحْتَاجُونَ إِلَى صَاحِبِ الْعِلْمِ فِي أَمْرِ دِينِهِمْ وَ لَا يَحْتَاجُونَ إِلَى صَاحِبِ الْمَالِ السَّابِعُ الْعِلْمُ يُقَوِّي الرَّجُلَ عَلَى الْمُرُورِ عَلَى الصِّرَاطِ وَ الْمَالُ يَمْنَعُهُ.


" ILIMI YA FI DUKIYA FALALA DA ABUBUWA BAKWAI; 


(1)- ILIMI SHINE ABIN GADON ANNABAWA, DUKIYA KUMA ABIN GADON MAGADA (ba kai za ta amfana ba). 


(2)- ILIMI BA YA QAREWA SABODA CIYAR DA SHI, ITA KUWA TANA QAREWA SABODA SHI (ciyarwar). 


(3)- DUKIYA TANA BUQATAR TSARO, SHI KUWA ILIMI SHI KE TSARE MA'ABOCINSA. 


(4)- ILIMI YANA SHIGA (har cikin) LIKKAFANI (yadda zai amfanar da mai shi a lahira), DUKIYA KUWA BARINTA AKE YI (a duniya). 


(5)- ITA DUKIYA TAKAN ISA GA (hannun) MUMINI DA KAFIRI, SHI KUWA ILIMI BA YA ISA (ga wani ) SAI GA MUMINI KADAI .


(6)- DUKKAN MUTANE NA BUQATUWA ZUWA GA MAI ILIMI CIKIN AL'AMARIN ADDININSU, AMMA BA SA BUQATUWA ZUWA GA MAI DUKIYA. 


(7)- SHI ILIMI YANA QARFAFAR MUTUM WAJEN HAYE SIRADI, AMMA ITA DUKIYA KUWA HANA SHI TAKE YI ."


_________________________

(1) و في نسخة: و أن أحبّ عبيدى إلى.


 


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 186


ALLAH YA SANYA MU CIKIN MASU NEMAN ILIMI FIYE DA NEMAN DUKIYA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

         (08126385470)


22nd Sep, 2020/ 5th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post