Harka Islamiyya A Najeriya A Mahangar Musulmi


 

Harkar Musulunci a Idon Masu Ilimi a Najeriya tana akan Mizani na Hatsari ga Mulkin Zalunci, Mulkin da a zahiri aka kirashi Mulkin 'Yan ci, da Fadar Albarkarkacin Baki Amma A badini Yazama Salon Mulkin Mallaka, Mulkin da ko Mulkin Turawan Mallaka Baikai Zalunci da Rashin Imani ga Al'ummar Najeriya ba.

Mulkin da Rayuwa da Dukiya da Kwanciyar Hankali Suka Kasa Samun Muhalli acikin kasa, Azzaluman Masu Mulki a kasar nan Sun maida Dukiyar kasa a matsayin kayan Gidan su, Kuma Basu Taimakon kowa daga su Sai iyalinsu. Ana iya Samun Mutum guda Mai Mulki daya yake iya yin Sama da Fadi da Dukiyar da Mutum Millions Zasuyi Rayuwa dasu da iyalinsu tsawon Rayuwarsu Amma Shi ya kwashe Shi kadai da iyalinsa kudin da Har Mutuwa Suke iyalinsu Su kasa cinye Dukiyar da Suka bari.

Dukiyar Najeriya tazama ganima ga Turawa Sai kashe 'Yan kasa akeyi Domin kawai a kore Mutane daga Yankunan su a Debi Zinare ko Man fetur.

A Haka Zakzaky, ya fito da tsarin da baya dagawa Masu Mulkin Zalunci kafa komai kankantar Zalunci Idan Zakzaky ya gani ko yaji Sai yayi Magana. Sheikh Ibrahim Zakzaky Malami Kuma Mai kokarin kawo Sauyin gyran Hali acikin Yan kasa da Rusa Gwamnatin Zalunci ta Najeriya Yana da Almajiran da Duk Wani Mai ilimi A kasar nan yayi Ittifaki akan cewa; Masu ilmi ne a Kowane Fanni na Kimiyyar zamani kama daga professors,Doctors,Sojoji,Yansanda Ma'aikata a kowace Ma'aikata a kasar nan Zakzaky na da Almajirai.

Yayin da Su kuma Sauran Mutane Al'umma kasa Gwamnati take cigaba da Bautar dasu da Jahilci ta hanyar Talauci da Kirkiran kungoyin Ta'addanci Domin Jefa Rayuwar Talakkawa Cikin Kuncin da Bazasu iya yin karatu ba, Balanta Asamu fata ta gyaruwa ko Hankalin Neman Mafita daga 'yan kasar.

A Karshe Masu ilimi a Najeriya na kallon Sheikh Zakzaky da Da'awarsa A matsayin Hanyar da idan Gamin Gambizar Kasashen Turai dake Rike da Sitiyarin Najariya Suna Juyawa, Sukayi Sakaci da Yunkurin da Sheikh Zakzaky yake yi, To Hakan na iya kawo karshen Daular Zalunci da ake Cigaba da Bautar da Al'umma Najeria tsawon Shekaru 60.

*Musa Hassan Shinkafi*

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post