@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADA KA KALLI ALQIBLA YAYIN BIYAN BUQATARKA
Ya zo cikin Biharul-Anwar game da abubuwan da Annabi (S. A. W. W) yayi hani a kansu. Ga su cikin riwaya kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
مَجَالِسُ الصَّدُوقِ، فِي مَنَاهِي النَّبِيِّ ص أَنَّهُ نَهَى أَنْ يَبُولَ رَجُلٌ تَحْتَ شَجَرَةٍ مُثْمِرَةٍ أَوْ عَلَى قَارِعَةِ الطَّرِيقِ وَ نَهَى أَنْ يَبُولَ أَحَدٌ فِي الْمَاءِ الرَّاكِدِ فَإِنَّهُ مِنْهُ يَكُونُ ذَهَابُ الْعَقْلِ وَ نَهَى أَنْ يَبُولَ الرَّجُلُ وَ فَرْجُهُ بَادٍ لِلشَّمْسِ أَوْ لِلْقَمَرِ وَ قَالَ إِذَا دَخَلْتُمُ الْغَائِطَ فَتَجَنَّبُوا الْقِبْلَةَ[8].
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج77، ص: 169
FASSARA
------------------
Majalisus-Sudduq cikin abubuwan da Annabi (S. A. W. W) ke yin hani a kansu.
Yayi hani mutum yayi fitsari qarqashin bishiya mai 'ya'ya ko a tsakiyar hanya.
Kuma yayi hani kada dayanku yayi fitsari cikin ruwa marar gudu (stagnant) , domin hakan kan jawo gushewar hankali.
Kuma yayi hani kada mutum yayi fitsari farjinsa na kallon rana ko wata .
Sannan yace, kuma idan kun shiga ba-haya (Gha'idi) kada ku kalli alqibla. "
(Biharul-Anwar, bugun Bairuit, J:77, Sh:169)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
11th Sep, 2020/ 23rd Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com