Gasar Mawaka: Shiga Ciki ka Rubuta Baity 5 A 'kasan Wannan Wakar (Comments) Da yafi Saura, Zaka Samu Kyauta Daga Alkalan Gasar idan Ankammala!!!



Bayan ka Rubuta Baity 5 din sai ka ajiye number ka!!!
______________
Amshi:- YAK'I K'ASAR MU KESO SUYI AMMA BA ZASU SAMBISA BA.
..
Birnin gwari zuwa . Zamfara  Dan musa ma basa je ta ba.
..
Ga 'yan ta'adda nacin karen su amma ba zasu yake su ba.
.
Boko haram da bandis nacan sun sa duban mutane gaba.
.
Barayi da masu yin garkuwa shegun ba zasu tarbe su ba.
.
Ya za'ayi muje mui fada makaman mu basu kai nasu ba.?
.
In an kashe mu d'an dakata iyalan mu sun shige fargaba.
.
In kuma dayan mu ya nakkasa hukuma ba zata kalle shi ba.
.
Yawancin mu gasu can na bara da maula ba'a kula tasu ba.
.
To mi yasa idan zaku yak'i 'yan shi'a ba kuyin fargaba.?
.
Ka ganka ka faye zolaya su  ba cikin dawa suke ba.
.
Mun san su gamu tare su lalle ba maji tsoron su ba.
.
Mata da yara ne maffiya yawan nasu ba muyin fargaba.
.
Tsofaffin su sun rike tasbaha matasa suna ta wak'e gaba.
.
A taron su babu mai bindiga balle mu kasa tarbar gaba.
.
'Yan shi'a suna da dadin kisa ba zamu kasa tarbar su ba.
.
In mun kashe a bamu kud'i da lambar yabo da girman gaba.

**Ina mawakan Kuzo asha ta'aliki**

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post