Buhari da karnukkan shi suka raba ni da Ishq Muh'd Suleman Innalillahi wa inna alaihin raji un sun kashe min Ishaq....!!
ALLAH SARKI SHAHEED ISAHAQ MUH'D SULEMAN.
Ma'asumah 🇳🇬Ng🇳🇬 News Update
✍️Shana islam✍️.
Da'sunan Allah ubangijin da ke zabar cancantantun bayin sa ya mai'she su Shaheedai a tafarkin Addinin Musululci tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammad (s) da iyalan gidan sa tsarkaka.
Yau Zanyi bayani dangane da Bawan Allah zabanben Allah a cikin bayin'sa wato Isahq Muh'd Suleman Sokoto Shaharanren jajirtancen marubucin nan a Shafin Ma'asumah Nigeria News update Nasan Ishqa muha'd da dadewa a soshiyal Midiya ina ganin rubuce rubucen shi sosai tun kafin fara aikin sa a'Shafin Ma'asumah tabbas na'karo da Ishq Muh'd Suleman ta fannin rubuce rubucen sa sosai saboda ganin kiyayewar shi wajen kawo labarin Gaskiya yasa na saka shi cikin Amintantun marubutan da Nike jiran naka sun kawo rahoto.
Mun fara ganin juna ne da Shaheed Ishq Muh'd Suleman A birnin Kano a wajen taron Mu'utumar na karawa juna sani da Shafin Ma'asumah ta shirya da yake mun riga shi isa a'muhallin nida Auwal m Tukur Muna Isa Muhallin Oga Dan masani Shankafi ya taso ya tarbemu cikin nishadi da walwala da jindadi muka aje jikunan mu muka gangaisa da sauran "yan uwa sai mukaci gaba da musha raka muna nan sai ga Shaheed Ishq Muh'd ya shigo isowar shi keda wuya waje ya barke da nishadi anata wasa da dariya ni kuma Duk da ban taba ganin sa ba ina ganin sa nace lallai wannan shine Dan uwan nan Ishq Muh'd Suleman Hakan ko ya tabbata bayan ya huta sai muka kama hira da shi muna wasa da dariya.
Bazan mantaba har na karbi wayar'sa ina kallo sai naga wani Vedio Wanda "yan salafiya sukayi na Mauludin Sahabbai Ganin wannan bidion ya kara jefamu cikin nishadi munata wasa da dariya Allah Sarki Shahed ishq Muh'd Suleman Baka fushi da abokin zama baka nuna bacin rai ko kadan.
Haka mukayi kwananki tare da Shahed Ishq Muh'd Suleman cikin farin ciki da sha'war zama da juna har muka kawo karshen Program Lokacin da akayi addu'a kowa zai kama gaban'sa Duk "yan uwa sun shiga juyayin rabuwa da juna sai na lura kowa yafi jin rabuwar shi da Shahed Ishq Muh'd Suleman nima naji a zuciya ta kamar kar mu rabu Amma ina ba yanda na iya ya tafi nima na tafi😭.
Tundaga wannan ranar Zumuncin'mu ya kara Haduwa muka shaku da juna yakan Kira ni a waya nikan Kira shi muyi wasa da da dariiya harma ba musan yanke waya Muna cikin Hakan Buhari da karnukkan shi suka raba ni da Ishq Muh'd Suleman Innalillahi wa inna alaihin raji un sun kashe min Ishq😭.
Yadda naji labarin halbin shi da Labarin Shahadar shi zanci gaba insha Allah ina fatan Allah ya karbi shahedar Dan uwana abokin aiki Ishq Muh'd Suleman.
@Shana islam.