.. FILM ƊIN YA TABA MUSULINCI NE ƘAI TSAYE –Cewar Zaharaddeen Mziag


 

FATAL ARROGANCE sunan film ɗin kenan a ƙarƙashin jagorancin wani Inyamuri kuma kirista (Chiristan) mai suna KINGSLEY OJI ANOSIKE ɗan jihar Enugu.  


Ba inaso infaɗi wani abu mai kama da ɓangaranci ba ko (Religionasm) ba, saboda ba tarbiyyar da Maulana Sheikh Dr Ibrahim Zakzaky ce ya bamu ba, kawai inaso inyi amfani da yaren ne domin zaifi sauƙin fahimta. 


Abin takaici ne da kuma cin mutumci kamar inyamuri kirista yashirya wani film ko ma rubutu da yashafi wasu musulmi, kuma saboda jahilci da toshewar basira wasu ɓangare na musulmi su marama abin baya. 


Kamar yanda wani bahaushe musulmi daga cikin waɗanda suka taka rawa a film ɗin yake cewa wai ba film bane da yashafi cin mutumci, a'a wai ana nuna abinda akayima malam ne na zalumci. 


To muɗauka ma haka ne, mi ya haɗa kirista da shiga abinda ba nashi ba? To balle ma gaskiya ba haka bane shi wan'nan film ɗin asali ma littafi ne aka rubuta a watannin baya da alƙalamin wani kirista maƙiyin addinin muslinci maƙiyin malam zakzaky da harka Islamiyya wanda aka ƙaddamar da shi a Abuja. Ga kaɗan daga cikin rahoto akan littafin wanda WITHIN NIGERIAN TA RUBUTA tun cikin watan janairu. 


("The Mission and vision of IMN show their disregard for the Nigerian state and deliberate intensions to overthrow the Nigerian government through violent means” he added.


The governor of Benue state, Samuel Ortom" who was distinguished guest of Honour at the event described the author, Terrence Kuanum as an astute young man who has survived many battles most of which were in the interest of the peaceful coexistence of Nigeria.) 


"Na ɗan tsakuro ne amma cin mutumcin yanada yawa" shi wan'nan littafin shine suke ƙokarin fassarawa a aikace, ta hannun waɗan'nan kiristocin da ɓatagarin musulmi da basu san addininsu ba. 


Don tsabar cin mutumci da raina addini sai suka miƙa shi kai tsaye a hannun waɗanda ba musulmi ba ta yanda zasu cimma dukkan ɓatancin da manufofin da sukeso su cimmawa. 


WANDA BAIYI IMANI DA LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI BA, 

Yau sune aka bawa kalmar Allah Arubuce (tutoci) suna ɗagawa da sunan Annabin mu a ciki, ta yiyu ma akwai najasa a jikin su, kuma sugama shooting ɗin su jefar da Sunan Allah ƙilan ma ataka saboda basu san darajar shi ba😭😭


Kai musulmi da kai nake! Musamman bahaushen Arewa, Idan har ƙiyayyar ka ga ƴan shi'a zaisanya kaji daɗi anɓata Malam Zakzaky da mabiyansa, to ai acikin ɓatancin sun haɗa da Allahn da kake bautawa da Annabin da kake girmamawa, Saboda mafiya yawa da sukayi wan'nan film ɗin lalataccin kiristoci ne da Addinin nasu ma yayi, Allah wadai dasu. 


Shin kayarda a taɓa Allah da manzo indai har za'a ɓata darajar malam zakzaky da mabiyansa? Idan kace Eh to bansan kai wane irin mujirimin mutum bane. Ko munafiƙi marabarka da kafuri, kace la'ilaha'illallahu abaki. 


SHIN MINENE LAIFIN MALAM ZAKZAKY A WAJEN KU NE? 

Malamin da ya tara mabiya sama da mutum miliyan Ashirin daga cikinsu babu ɗan boko haram, babu mai garkuwa da mutane babu ɓarawo babu ɗan giya balle mashayin kwaya shine kuke so kuɓatawa suna har kuna taɓa shaksiyyar manzon Allah(S) wajen kokarin ɓatamasa?


Shin yadace kuɓatawa wanda silarsa miliyoyin mutane suka shiriya, suka maida imaninsu ga Allah duniyar ma bata shamasu kaiba, balle a iya samun ƴan kidnapers masu kashe mutane saboda son duniya acikinsu? 


WANE MALAMIN KUKESO KUJEFA MA KALMAR TA'ADDANCI? malamin da yana cikin aminci da iyalansa da Almajiransa suna karantarwa sama da shekaru arba'in kuka dirar masa da kisa babu ƙaidi babu ji babu gani, saida kuka kashe sama da mutum dubu, gami da ƴaƴansa, kuka kutsa cikin iyalansa kuka buɗemasa wuta dashi da matar sa san'nan kuka kamashi da harsasai ajikin sa kusan shekara shida har yau baku bari ammasa magani ba kuma baice maku ko Allah ya isa ba shine kuke cema ɗan ta'adda.😭😭


WAI SHIN WANENE ƊAN TA'ADDA A WAJENKU, WANDA AKA KASHE KO WANDA YAYI KISA? Tundaga shekarun baya na mulkinku har zuwa yau kashemu kuke, kisa mafi muni babu babba babu yaro ba mace babu tsoho, kullum kamamu kuke kuna ɗaurewa gami da azaba mafi tsanani, amma har yau inda ake bamu taɓa ɗaukar makami mukace zamu rama ba, duk da munada zaratan matasa marasa tsoro da zasu iya ɗaukar ko wace irin fansa amma bamuyi ba. 


KUNE ƳAN TA'ADDA AMMA DA TSIYA SAI KUN MAIDA FARI YA ZAMA BAƘI DUK DA BA KALAR SA BACE. Kunyi rinin amma kalar taƙi canjawa kun gayyaci kwararrin maruna(karofi) Sunzo sun nuna ƙwarewar su, sun sanya BA-BA da Toka, har katsi, sun sanya amma dai kalar bata canja ba, to yanzu kuna ganin akwai wani ƙazamin kirista ko ruɓaɓɓen musulmi da zai iya canja kalar?  


Tsabar ta'addancin ku yana nema ya kaiku ga hauka. Bayan kisa da kuketa yi baji ba gani kuma har wayau kunje kotun ku a tsakar dare kunsanya wata ruɓaɓɓiyar kirista wai ita alƙaliya ce, ta ayyana harka a matsayin aikin ta'addanci, kuma tayimaku yanda kuke so amma haryanzu baku gamsu da sunan da kuka ƙirƙira ba, saboda ku kanku kunsan ƙarya kuke. 


Munkaiku kotu mun tandaraku da ƙasa yafi sau'shurin masaƙi, anya ɗan ta'adda yana nasara a kotu kuwa? Nazata ɗan ta'adda duk inda yake hukuncin kisa ne akansa, to miyasa muke liƙaku da ƙasa a shari'a? 


BANTAƁA TUNANIN BASIRAR KU TA ƘARE A FILM BA. 

Ashe baku iya wasan? To ku yada kari mana kuhuta! kunemi sulhu ko dan kudaina ɓannata dukiyar kasa wajen shuka dutse. 

Kuɗin da kuke kashewa wajen ɓata harka da aikin ƙasa kukayi da yanzu talaka yasan inda aka dosa. 


Kuntara jahilan farfesoshi da daƙiƙan malamai kun basu miliyoyin kuɗi kun raba masu aiki na buga litattafai da rubce rubuce da sunan yaƙi da shi'a amma duk sanda kukayi wauta sai mutane sugane gaskiya, anya kuwa? Ashe bazaku sanya hankali ba(idan kuna dashi) 


Tallar da kukayi mana har duniya ta sanmu, gami da tonama kanku asiri da kukayi har duniya tagane kune ƴan ta'adda idan da mu zamuyi wallahi bamu da kuɗin da zamu iya wan'nan aikin. 


Ya isheku kugane cewa duk'sanda kukayi wani taddanci sai mutane suƙara fahimtar harka, yanzu gashi tashiga gidan kowa har cikin ɗakunan kwanan ku, ƴaƴanku ma dayawa wasun su sunfahimci harka, wasu kuma sungane ku ƴan tadda ne. 


Haka wan'nan film ɗin shima zakuyi kugama ƙarshe ayimaku dariya duniya ta ƙara fahimtar ku wawaye ne jahilai ne ƴan ta'adda.  


YAKUB MOH'D. Ka kwashi sama da shekara Ashirin kana harkar film ana ganinka a matsayin mutumin kirki ka taka rawa iri-iri sunanka yaje duk inda ba'a zato amma yau katashi a ziro, miyasa bakayi tunanin cewa ana barin Halas ko don kunya ba,? Inji bahaushe. 


Shin sunan ne bai isheka ba kakeso ka ƙara da baƙin suna, kokuwa kwaɗayin duniya ne? Ko kuma kwakwar film ne, don ace kafito a wani mashahurin film? Bana tunanin kwakwar film ne saboda wace irin kyamara ce baka gani ba? 

Sai dai ince kwaɗayi da son abin duniya ne ya kaika ga goran da babu fafi, har kanuna baka damu da addinin ka ba akan kuɗi. Akan kuɗi ma za'a iya taɓa Allah da annabi kaidai idan Aljihunka ya cika ina ruwanka. 


Babu mamaki ma a gabanka har alƙur'ani sun ɗauka duk da kasan ba musulmi bane illa iyaka kace duk cikin shutin ne, to tunda har sun ɗaga tutoci masu la'ilaha illallah a gaban ka kuma ka tayasu mike bazasu yi agabanka ba kayi shiru? 


To dai abinda zance maka kaji tsoron Allah saboda ina ganinka har yanzu a matsayin musulmi, kuma kasani ba malam zakzaky kuka cima mutumci ba Addinin ka ne ka tozarta, bayan haka kuma mu, a gurin mu kashiga babin tunawa da maka addu'a cewa abinda kayi Allah yayimaka. 


Naji kace ba kai kaɗai bane musulmi daga arewa amma dai kaine wanda fuskarka ta fita aka sani, sai kuma ka manta da sanayyar da akai maka ka aikata kuskure bakayi tunanin ƙalu balen da zai biyo baya ba, saboda haka kaine wakilin sauran wataƙil ma kai kakaisu. 


Don haka kusaurari Allah. Idan baku tsoron Allah kusaurari kotu. 


Malam zakzaky dai Hasken Allah ne makirci kisa kamu ɗauri da yin finafinai a kansa baya canja masa suna. 


Mu kuma mabiyan sa munan nan akan inda ya barmu, mu addini muke iya fahimtar mu kuma doka ta bamu dama, babu kuma abinda zai canja, abinda kukayi a baya bai sanya muka ɗauki makami ba, don kun nuna mu da makami a cikin film ansan ƙarya kuke saidai kawai acemaku, gaskiya kun iya sharri. 

Don haka akafta muga mu da ku waye boss waye actor, Afilm dai munsan Boss Azzalumi ne Actor kuma mazlumi (mai kwatar ƴanci).

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post