@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Yazo cikin hadisi daga Manzon Allah (S. A. W. W) yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
عُثْمَانَ الْعَبْدِيِّ عَنْ جَعْفَرٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَلِيٍّ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص
" لَا قَوْلَ إِلَّا
بِعَمَلٍ وَ لَا عَمَلَ إِلَّا بِنِيَّةٍ وَ لَا عَمَلَ وَ لَا نِيَّةَ إِلَّا
بِإِصَابَةِ السُّنَّةِ. "
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 208
FASSARA
" MAGANA (ba ta amfani) SAI DA AIKI, SHI KUMA AIKI (ba ya yiwuwa) SAI DA (kyakkyawar) NINYA, (haka kuma) BABU AIKI BABU NINYA SAI SUN ZO DAIDAI DA SUNAR ANNABI (S. A. W. W) ."
SHARHI
---------------
Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, surutu ba ya amfanarwa har sai an hada shi da aiki, da za muyi tayin surutu kan wani abu da muke son cigabansa matuqar bamu hada shi da aiki ba to ba zai yiwu ba.
Sannan ko da ace munyi magana tare da aiki matuqar babu kyakkyawar ninya cikinsa ba zai amfanar damu ba.
Haka kuma da za muyi aiki tare da kyakkyawar ninya sannan ya zamana ya sabawa sunnar Annabi (S A. W. W), to, da ba za mu sami lada cikinsa ba, tamkar dai wanda ya aikata kyakkyawan aiki ne da mummuniyar ninya ba zai sami lada ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
10th Sep, 2020/ 22nd Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com