Duk wanda yacemini Shugaba Muhammadu Buhari mai gaskiya ne to yazama mugu mara imani – Zaharaddeen Mziag


Yanzu waɗan'nan alƙawullan basu isa sumaida Buhari da jam'iyyarsa maƙaryata ba?  

Kai maiganin Gwamnatin APC da Buhari masu gaskiya don Allah daga cikin su wanne akacika? 

Wane alƙawari yacika wanda yanzu talaka yake mora?  

Idan zakayi adalci ko baka bayyana arubuce ba cewa ansaɓa alƙawari zaka faɗa azuciyarka cewa tabbas Baba Buhari baicika alƙawari ba. 

To madallah da wan'nan amsa taka, don haka amatsayin ka na musulmi nima musulmi Shugaban da kake so wanda yake al'ƙawari ya saɓa shima musulmi, kuma galibin masoyansa musulmi, dole ne inkafa hujja da ayoyin al'ƙur,ani da hadisin manzo Allah (ﷺ)duk wanda yaƙi yarda da abinda zanfaɗa don son zuciya ko soyayyar wani wanda baya son sa to sai muce wal'iyazu billah ko bakabar musulinci ba ka fidda kafar hagu,da hannun dama daga cikin da'irar musulinci, kuma Allah s.w.t yana cewa acikin suratul baƙara aya ta 208 
بسم الله الرحمن الرحيم. 
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا ادْخُلُوا فِي السِّلْمِ كَافَّةً وَلَا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ ۚ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ
Fassara
Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyananne. 

Allah ka kiyashemu taɓewa duniya da lahira. 

Allah Mai Girma da Daukaka yake cewa:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفْعَلُونَ )

Ya ku waɗanda suka yi imani! Don me kuke faɗin abin da ba ku aikatawa?

( كَبُرَ مَقْتًا عِندَ اللَّهِ أَن تَقُولُوا مَا لَا تَفْعَلُونَ )

Ya girma ga zama abin ƙyama awurin Allah, ku faɗi abin da ba ku aikatawa.

(Suratul Saff (2-3)

A bayanin (tafsir) wadannan ayoyin Sheikh Maududi yace:

Ɗaya daga cikin ma’anar wannan ayoyi shine yakamata a samu cikakkiyar yarjejeniya tsakanin kalaman Musulmin gaskiya da aiyukansa: yakamata a aikata abinda yace ze yi, idan kuma bashi da niyyar yi, ko kuma bashi da ikon yayi to gwara kar ya faɗa cewa ze yi. Ko yace abu kaza yayi akasin waninsa, wato idan yayi zance sai ya canza.

Manzon Allah (ﷺ) yayi bayani cewa wanda ya siffantu da irin wannan ɗabi’a to alamace ta cewa shi ba cikakken mumini bane sai dai munafuki. A wani hadisin yace: “Alamar munafiki uku ne, koda yayi salla yayi azumi yace, shi musulmi ne: Idan ya yi zance, sai ya yi ƙarya, kuma idan yayi alƙawari, sai ya saɓa, kuma idan aka amince masa sai ya yi ha’inci.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.‛)

A wani hadisin yace: Abubuwa huɗu wanda ya kasance cikinsu ya zamo tsantsan munafiƙi. Wanda ya kasance yana da yankin ɗaya daga cikinsu to ya kasance yana da yankin munafinci tare dashi, har sai ya barta (a) Idan yayi magana zai yi ƙarya. (b) Idan yayi alƙawari zaiyi yaudara. (c) Idan yayi wa’adi ya saɓa. (d) Idan yayi husuma (faɗa) ya fajirce (yaƙi haƙura)‛. (Bukhari, Muslim).

Malamai kusan gaba ɗayansu suna kan fahimtar cewa idan mutum ya jingina ga Allah misali yaci alwashi zeyi wani abu, ko yayi yarjejeniya da wasu, ko yayi alkawari da wani ze yi wani abu, to wajibi ne dole ne a kansa ya cika su, sai dai idan abinda yayi alkawarin dashi zunubi ne. Idan kuma zunubin ne, to kada ya cika alwashin ko alkawarin, amman sai yayi kaffara kamar yadda Aya cikin Suratul ma’ida tayi bayani.

(AI-Jassas da Ibn al’Arabi, Ahkam al-Qur-an an). [Duba: Tafheem Al-Quran ns Sheikh Abul A’la Moududi].

Tabbas Allah ya tanadi azaba mai girmawa munafukai a wurare da dama cikin Qur’ani, kuma babu masifa da bala’i irin wannan. Kamar ayata 145 cikin suratul Nisa’i da sauransu. Ya Allah ka tsare mu da Munafunci da Munafukai da siffofinsu 
 
Munafincin na APC da Shugaba Buhari bai tsaya nan ba sai ya kuma tsananta ma talakawansa waɗanda yakewa jagoranci. 

Yau anwayi gari mutane na mutuwa da yunwa da annoba ga musifar zubda jini wanda kuma duk munsan hukunci sa a addini. 

Kada intsawaita idan fushin Allah ne ya sauka a ƙasar mu har Allah ya jarabamu da Buhari Allah muntuba Allah kayafe mana. Allah kabamu mafita, anan duniya kacanja mana mafi alheri ba don halin mu ba, alahira kuma Allah kaimana kyakyawar cikawa da imani.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post