DU GIRMANSA AMMA YA TSAYA A HAKA –An Cewa Buhari Kudin Buhun Dawa Yakai Naira 23,000



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Shi dai talaka babu abinda yafi yawan mu'amala da shi a matsayin abinci fiye da dawa da masara. 


Wadannan nau'in abinci kala 2 sune ake sassarrafa su ko jijjuya su zuwa yin abinci kala-kala . Misali :-


Tuwo, 


Dambu, 


Gwate, 


Kunu, 


'Danwake da kuma 


Masa. 


Idan ka kasa manoman wannan qasa tamu Nigeria zuwa kashi 100 za ka tarar kashi 80 daga cikinsu ba sa iya noma abinda za su ci a shekara, dole sai sun shiga kasuwa suna sayen dawa da masara daga hannun masu kudin da suka saya suka ajiye, ko daga hannun manyan manoman da suke yin noma a matsayin hanyar samun kudi. 


Sakamakon kamfen (campaign) da Buhari yayi wanda ya riqa furta samawa talakawa abin more rayuwa da sanya su cikin farin ciki 🕺🏻👯🏻‍♀️da walwala yasa talakawa yin cincirindo wajen fitowa su kada masa quri'a don cimma wannan buri, ashe kuma ba anan take ba !


Zuwa wannan lokaci dai talaka ya nutse tsundum cikin bala'i da quncin rayuwa sakamakon hauhawar komai na rayuwar dan'adam. 


Wannan dalili yasa suka kai kukansu 😢 😢 😢 zuwa gare shi (Buhari) suna nuna masa cewa bala'i yayi bala'i, yanzu kudin buhun dawa ya kai #23,000 maimakon yadda aka riqa sayar da shi a farashin #7,500 a kaka. 


Abinda ya fito daga bakinsa shine; 


" DU GIRMANNAN NASA AMMA YA TSAYA A #23,000 ?"


tunaninsa shine, buhun sugar dana fulawa dana shinkafar gwamnati bai kai na buhun dawa ba amma ai ya fi shi kudi, kamata yayi ace na dawa ya fi su kudi tunda ya fi su girma !


WAYYO TALAKAN NIGERIA !!!


😜😂😝😋😀😨🤥🥱😪💀☠️


Tare da Ado Isah Guda. 


      09039791509


8th Sep, 2020/ 20th Muharram, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post