Don Kyautata Duniyar Ka Da Lahirar Ka: Annabi (S) Ya Hore Mu Da Kasancewa Tare Da Mutane Uku



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED

A matsayinsa (S. A. W. W) wanda ya zama abin koyi kuma mai saita qwaqwalen al'ummarsa don su kasance masu rabauta a duniya da lahira bai barmu kara-zube ba sai da yayi mana irshadi kan wadanda ya kamata muyi mu'amalarmu dasu don kyautata rayuwarmu ta duniya da lahira. 


Ya zo cikin hadisi inda yake cewa ;


" KU TAMBAYI MALUMA, KUYI MU'AMALA DA MASU HIKIMA, KUMA KU ZAUNA TARE DA FAQIRAI. "


       (Tuhfatul-Uquul, Sh:34)


                DARASI 

              -----------------

darusan da za mu dauka cikin wannan hadisi sune ;


(1)- Duk wanda zai riqa tambayar malami (ba jahili ba), to, a kullum zai riqa qaruwa da ilimi da kuma qara neman kusancinsa ga Allah. 


(2)- Yin mu'amala tare da masu hikima na hana muyin aikata abinda zai zo yana yin da-na-sani daga baya, sannan shima zai kasance mai hikima abin koyi ga mutane. 


(3)- Zama tare da faqirai (mabuqata) na ragewa mutum girman kai, sannan za afi amfanuwa da shi fiye da wanda ya nisance su ya kasance abokanan zamansa sune masu kudi ko masu mulki. 


Duk wanda ke zaune cikin jama'a ya fi tausayinsu da taimakonsu fiye da wanda ba ya cikinsu.  


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


          09039791509


3rd September, 2020/ 15-2-1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post