Da yawan lokuta mutane sukan ce Yan SHI'A basu Yarda da sahihul bukari da musulimba, duk da cewa duk abin da ke cikinsa sahihai ne. A matakin farko Yan Shia ba suce duk abin da ke cikin sahihul Bukhari da musulim karya ne ba, face abin da suke magana shine, duk duniya babu Wanda zai rubuta littafi ya ce babu kuskure in banda alkurani.
Dalili na farko akwai hadith da yawa Wanda Bukhari ya karba, daga Wajan Makasa Yayan annabi Wanda duk duniya babu me musu sun kashe Yayan annabi, hasalima su da Kansu a tarjama sukan ce wane shi kace Yayan annabi Amman sukane babu kunya babu tsoran Allah.
Mudauki misali na farko kwamandan da ya Jagoranci kashe Imam Hussain (as) a Karbala Umar Dan sa'ad a tarjama sukace shi ya kashe Hussain Amman sikane.
Abin tambaya da bakin ciki a nan Yaya Wanda ya kashe Yayan annabi (Sawa) Amman ace sukane tare da cewar annabi (Sawa) shi da Kansa ya koka Akan kashe Dan sa Hussain Amman Yan wayi Gari Makasan Yayan annabi an koma Ana karbar hadith nasu. Mu dauka cewa Wanda ya zagi abubakar da Umar da USman ko Wanda suka kashe USman Kuna Zatan Bukhari zai Karbi hadith nasu ko da wasa? Kai Bama da kisaba A'a da zagima a ce suna zagin wadannan bayin Allah Bukhari ba zai Karbi hadith nasu ba, shin da wannane dalili Bukhari zai Karbi hadith Wajan wadanda suka kashe Yayan annabi?
Abu na biyu, hasalima Wanda ya kashe Imam Ali Abdurramani bin muljim almuradi, Shima an Karbi hadith nasa, shin ko da akwai Wanda zai kawomana hadith guda daya tak da Bukhari da musulim suka Karbi hadith a Wajan Makasa USman ko Umar?
Na uku Marwan Bin hakam Wanda duk duniyar musulimci babu me musu annabi ya tsine Masa alabarka su da bakin su Amman sun Karbi hadith nasa, Kai Bama tsinewa ba Har korarsa MA sai da annabi yayi daga Garin madina ko kunsan Karshema Bayan wafatin annabi Har gwamna aka bashi? Amman Buhari ya Karbi hadith nasa, Kuma su suka tabbatar da ba Kunansu.
Abu na hudu, dauki Abu hurairai Wanda ko Shekara Bai yi da annabi ba manzan Allah yayi wafati Amman yafi kowa hadith a Bukhari, kididdigar da Kayi hadith na Sayyidina Ali (as) ko 40 ba sukaiba na Matar sa Sayyida Zahara (Ah) ko goma Bai kaiba, a cikin hadith da bukari ya rawaita Sama da dubu 5, mudauka wadannan ma, Baza su Karbi Addani daga Gare suba, shin Ina Sahabban da akaci wahala da su tun farkon Addani babu irin wahalar da basu Shaba, irin su Bilal, Ammar, Huzaifa, mikidar, da sauran su, shin hadith na wane dasu a cikin Bukhari da musulim? Idan addini ake bukatar samu Wajan wadannan za a tambaya, Amman ga badaya ko Shekara 3 Kai 5 Abu hurairai Bai yi da annabi ba Amman yafi kowa yawan hadith sai.
Abu na biyar a Bukhari akwai hadith na taba Darajar manzan rahama (Sawa) marasa dadin ji Wanda mu kaddara su abubakar da Umar da USman aka dangantawa da sun rika tsinewa Malamin da ya rawaici wannan ruwayar misali
Dauki hadith abuhurarai a Bukhari hadith me lambar 2143. Abu hurairai ya rawaito cewar Wai annabi yace, shedan in banda Dan Maryam Har zuwa Karshen hadith din. A hadith ya Nunacewar hatta annabi shedan Yana suka ban da Dan Maryam Kayi alkalanci me ake NUFI. Duk me hankali a nan Nunamaka annabi isa gaba yake da MANZAN RAHAMA (SAWA).
Dauki hadith na 3 a kitabul ba'adul wahayi, babi na uku, Yana cewa Bayan anyiwa annabi wahayi a Kaishi Wajan pastor sannan ya tabbatar da cewa shi annabi ne, HAR zuwa Karshen hadith, wani abin takaici hatta kiristoci naga suna Kalubale tar musulmi akai suna cewa ya za ayi abi mutumin (w) da baisan cewa shi annabi bane aka ran Kansa? Sai da akaje Wajan wani? Hasalima akwai kiristan da ya tambayeni Wai da gaske ne haka ta faru nace dashi karya ce kawai maganar Bata in Gantaba Har nake tambayar sa a Ina yaji wannan mgnar ya Nunamin cewar malumansu su ke Karanta musu. Haba ya al'ummar musulmi kuyi tunanini mana? Su a nabawa tun rangini tun ran Zane, Babu wani annabi da Allah ya turo baisan cewa shi annabi bane sai da akaje Wajan wani ya tabbatar Masa babu ko daya Ballantana cikamakin annabawa Wanda babu kamar sa kaf duniya da lahira Amman baisan cewa shi annabi bane sai da yaje Wajan wani Malamin kiristar.
Dauki hadith 5796 juzui na 7 kitabul libas, hadith na cewa Wai lokacin da annabi zaiyi wa ubaiyu Dan salul sallah Bayan ya mutu sai Umar ya jawo Rigar annabi tabaya yace ba Allah ya hanaka yiwa munafikai sallah ba Wai sai ga Aya ta sauka Har zuwa Karshen hadith me ake Nunamaka annabi Allah na hanashi Abu Amman yanayi Har Sahabbai su tuna Masa Kuma Yana Mantawa da Abu, idan harko za Asami wani daga cikin annabawan da Allah ya turo suna Mantawa da sakon Allah to ya matsayin sakon da Allah ya aikosu da su, haka Kuma idan Har za a samu wasu su tuna musu to su ya Kamata Allah ya turo.
Sahihul Bukhari juzui na 2 kitabul Amali fissalat 1610 me hadith ke cewa Wai annabi idan Yana sallah shedan na bujuromasa Inji Abu hurairai Har zuwa Karshen hadith, karda ku manta sunce Umar Dan kaddabi shedan baya hada hanya da shi, Amman annabi Allah Yana sallah Ibada me girma kamar sallah Kuma mafi girma a annabawa Amman shedan na bujuromasa, me ake nunama ka Anan Umar yafi annabi Daraja domin shi shedan baya hada hanya da Umar Amman annabi ba haka bane shedan ya raina annabi idan Har za a samu wani annabi daga annabawan Allah shedan ya raina she me zai Hana a turo Wanda shedan bazai raina Shiba?
Mu Duba hadith Bukhari juzui 4 kitabul jahad wasiyari hadith me lamba 2789 ruwayar Anas sukace Wai annabi na zuwa gidan ummu harmin bint Milhan ta na ciyar da annabi abinci da yaci ya koshin sai yayi bacci ya Kwanta tasa Hannunta Kansa tana shafa Kansa, HAR yayi bacci, Karshe ya tashi daga bacci Yana murmurshi Sabo da wani mafarki da yayi.
Mukaddara wannan maganar Yan Shia ne suka Dan Gantawa Umar ko abubakar ko USman da Kaji tsiniwa da zagi Kai Karshema sai a fitar da mu daga musulimci Amman sun dangantawa annabi Matar aure annabi yace yaci abinci yayi bacci tana shafa Kansa Karshe Har yayi mafarki ya tashi Yana murmurshi WANNAN WANNE IRIN ISKANCINE? ko yaushe a na nunama al'umma cewa annabi Mayan Matane ko ubanka aka da ka tawa wannan Kai kasan anci Zarafinsa Ballantana MUHAMMAD RASULLAH (SAWA) WANNAN ISKANCI HAR INA,? ya Kamata maluma su dauki wannan sallan su rinka zuwa gidan Matan wasu suci abinci suyi bacci Matar gidan ta rinka shafamasa Kansu Amman ga maluman da suka yarda duk abin da ke cikin sahihul bukari sahihai ne domin Allah yace muyi koyi da annabi Sawa)
Haka Kuma kuduba musulim juzui na 5 kitabul Nikahi babi na 2 hadith me number 1403 sunce Wai annabi yaga Wata tsaleliyar mace Yana tare da Sahabbai ya rugu da gudu yaje yasa du da Matansa Har zuwa Karshen hadith yafi to Yana fada musu wance ya afkawa. INNALILAHIWA.... ANNABIN ALLAH. KAI BAMA ANNABI BA A'A MUTUM GAMA GARI NA KIRKI ZAI RINKA KALLAN MATAN MUTANE HAR YAJE YA AFKAWA MATARSA KARSHE YAZOO YANA FADAWA ABOKAN SA?
YAU MUKADDARA WANNAN MAGANAR YAN SHIA NE SUKA FADAWA WANI DAGA SAHABBAI DA KUNJI YADDA DUNIYA ZATA CIKA DA ZAGI DA AIBATAWA.
Irin wadannan ruwayoyin suna da yawan gaske, ta Yaya zamu yarda da sahihul bukari muce komai sahihai ne, tare da cewar Yayan annabi Yaki rawaitar hadith daga Gare su sai Makasansu Sabo da suna da mulki a yau maluma su Gayamana hadith Imam hassan da Hussain Imam Jafar duk duniya babu me musun Yayan annabi ne hadith na wane a cikin littafin su? Kai Hasalima Imam Jafarsaddik ko daya Bai rawaitaba Amman Kashi Makasansu sun rawaici hadith su, wadanda annabi ya tsinwama su da Kansu suka in Ganta Amman sun Karbi hadith nasu. Ya rabbulamin Anya kuwa mutanan sun yarda da annabi manzan Allah ne?
Wadannan sune DALILAN a takaice da ba mu yarda da bukari da musulminba shakka babu akwai hadith annabi Amman mafi yawa akasin maganar annabi ne.
Wassalamualaikum....
By Habibu Rabiu Nasrallah.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com