@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHI MA KANSA YANA ZARGIN KANSA
Abinda ya tabbata cikin ingantattun riwayoyi na littafan tarihi shine, Abu Huraira na daga cikin wadanda suka muslimta a baya-baya, domin shekaru 2 kacal yayi tare da Annabi (S. A. W. W) bayan muslimtarsa.
Wani abinda ke daurewa mutane kai shine, me yasa yafi kowa yawan hadisai alhali akwai wadanda suka zauna tare da Annabi (S. A. W. W) na tsahon shekaru 23 amma ba a riwaito hadisai masu yawa daga gare su ba ?
Abu Huraira ya bada amsar wannan tambaya cikin hadisin da ke biye.
👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽
Daga Abdul-Azeez Bn Abdullahi yace, Malik ya bamu labari daga Ibn Shihab, daga A'araj, daga Abu Huraira yace,
" Lalle mutane na cewa Abu Huraira ya yawaita (hadisai) , ba dai don ayoyi biyu (2) cikin littafin Allah ba da ban bada labari ba. " Sa'an nan ya karanta;
" LALLE WADANDA SUKE BOYE ABINDA AKA SAUKAR NA DAGA HUJJOJI DA KUMA SHIRIYA....... "
(Baqara, aya ta 159-160)
Yace, " Lalle 'yan'uwanmu daga Muhajirun sammakonsu zuwa kasuwanni na shagaltar da su. Su kuma 'yan'uwanmu na Madinah (Ansar) ayyuka ne kawai ke shagaltar dasu cikin dukiyoyinsu.
Abu Huraira kuwa ya kasance yana lazimtar Manzon Allah (S. A. W. W) (a ko da yaushe) cikinsa a qoshe, kuma yana halartar guraren da su ba sa halarta, sannan yana kiyaye abinda su (Sahabbai) ba sa kiyayewa. "
(Bukhari, hadisi na 118)
Abinda yake tabbatarwa anan shine, shi ya fi dukkan Sahabbai kasancewa tare da Annabi (S. A. W. W), sannan ya fi su kiyaye abinda suka ji daga Annabi (S. A. W. W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
8th Sep, 2020/ 20-1-1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com