Dalilan DaYasa Sayyid Zakzaky (H) Ke Kebe Yan 'Yan Shi'a Da Wani Ilimi


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KOYI DAGA ZANTUKAN IMAM ALI (A. S) 


Ilimi wata amana ce daga Allah wacce ya dorata kan maluma, kuma ya umarce su dasu sanar da shi ga wadanda basu sani ba. 


Babban laifi ne ga wanda yasan wani ilimi ko shiriya sannan ya boyeta ga wadanda basu sani ba. 


Sau da yawa za ka iya sanin wani abu na ilimi wanda zai amfanar da kowa, amma sai kaga an sanar da wasu mutane a kuma boye shi ga wasu don wata maslaha. Idan kace duk abinda ka sani za ka bayyanar da shi, to, zai iya zama fitina ga wasu maimakon ya zama shiriya. 


Wannan dalili yasa Manzon Allah (S. A. W. W) ya riqa kebe wasu mutane daga Sahabbansa yana ilimantar dasu daga abinda ya sani, kuma ya bar wasu ba tare da sun sani ba. 


Sayyid Zakzaky (H) ya yi koyi da shi, domin ilimin da yake bayyanar da shi cikin 'yan shi'ah (KHASS) a Husainiyyah Baqiyyatullah ba ya bayyanar da irinsa ga wasu wadanda ba 'yan shi'ah ba. 


Iman Ali (A. S) na cewa ;


👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽


" KU BAWA MUTANE LABARI DA (irin) ABINDA SUKA SANI (Wanda qwaqwalwarsu za ta iya kamawa), KO SO KUKE SU (mutanen) SU QARYATA ALLAH DA MANZONSA (S. A. W. W) ?"


(Bukhari, kitabul-ilmi , babi na 50).


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


               08137925034


10th Sep, 2020/ 22-1-1442

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post