من أقوال الإمام علي عليه السلام:
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HIKIMA KAYAN MUMINI
Cikin zantuka na Imam Ali (A. S) yana cewa ,
" من توكل على الله غني عن عباده ."
FASSARA
------------------
" DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH WADATACCE NE DAGA BAYINSA ."
Abinda wannan magana ta hikima ke koyar damu shine, duk wanda ya dogara ga Allah ba da buqatuwa daga waninsa, domin shine mai iko akan komai.
Shi kuwa wanda bai dogara ga Allah ba yakan wadatu ne daga wasu a matsayin wadanda za su iya yi masa maganin komai.
Idan muka kalli jagoran harka islamiyyah Sayyid Zakzaky (H) bai damu da taimakon wasu ba, domin shi ga Allah ya dogara, kuma shine ma'ishinsa akan komai.
Irin haka ya kamata sauran al'umma su kasance, wato masu dogaro ga Allah kan komai ba dogaro ga wanin Allah ba.
Hakan shi zai bawa mutum izzah da kwarjini wajen azzaluman shugabanni da miyagun masu hannu da shuni.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
9th Sep, 2020/ 21st Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com