CIGAGA DAGA KASHI NA FARKO,
Hijabin ta na Riqe a Hannun Shi ya Rike kamar Igiyar Shanun Ginsamin Salla,Sai take Tunanin abinda Zatayi ta Kubuta daga Abinda yakeso Yafaru da'ita,Tana Tunanin Yi Mishi Ihu ko Kururuwa ko kiran akawo Mata dauki Sai a Lokaci Guda Tana Tunanin abin Zai Iya Munana,Don Ita Yarinya ce Mai Qiima da Daraja a idon Mutanen da suka Santa alfarmar Mahaifin ta Sananne na a Tsakanin Al'ummar Garin,
Ana Haka Zuciyar ta Taraya Mata tace Masa Don Allah Abin Watarana Yana Tafiya Yaga Wani Yana yiwa Mahaifiyarsa Kwatankwacin Abinda yake Mata Ya Zaiyi da Mutumin Kuma Ya Zaiji a Ransa,Kuma ya Zai dauki wannan Mutumin daga Ranar ???
Sai Taga Rashin Dacewar fada Masa Hakan,Saboda da Yiwuwar ma Mahaifiyarsa batasan yazo Wurinta ba ballantana tayi Tunanin aikata hakan daga Gareshi,
Sai Zuciyar ta ta Raya Mata cewa tafadi Masa Idan Wata Rana Yaga Wani Saurayi Yana Rike Da Hijabin kanwar sa ya Zaiyi Dashi Kuma ya Zaiji a Ransa,Aiko Taake Tafada Masa Hakan,Kawai Sai yace Mata Gaskiya Bazai ji Dadin Hakan ba,Sai tace to miyasa Ita Zai baro Garin su Yazo Yasame ta a Garin su yayi Mata Haka????
Kawai Sai Yasakar Mata Hijabin,yasa kansa a kasa Saboda yarasa amsar Tambayar ta,Bata Iya Fada Masa komi ba Sai Allah Ya'isa Bata Yafe Mishi ba,Saboda Tace Masa a Rayuwar ta A Tsakanin Mahaifi da Mahaifiyarta Kannai da Yayyen ta ba Wanda Yataba Kaama Mata Hijabi ya Cukuikuye Yadda Yayi Mata,
Nan Take Tace Masa Taa Fasa Rakashi Gidan Kawar shin Kuma Kawarta,Sai Tajuyo tadawo Gida,Saita barshi a Wurin da abin Yafaru,Tana Dawowa ta Zauna Tana Tunanin Wannan Abin Daya Faru Da'ita Cike da Bakin Ciki da Takaici da Damuwa,Ana Haka Sai Mahaifiyarta ta kirata Saita amsa Ta fita donjin mai mahaifiyarta zata Fada mata,tana zuwa ta Duuqa Kasa ta Sunkuyar da kanta kasa Tana Jiran Mai Mahaifiyarta Zata Fada Mata,Sai Mahaifiyarta Taji Tana Sheshsheka Sannan Tayi Ajiyar Zuciya,Sai Mahaifiyarta tace Wance {Ta Kira Sunan ta}Sai tace Lafia kuwa ???Sai Yarinyar tace Lafia Mama, Sai Mamar tace Naga Bansaba Ganin ki a Wannan Yanayin ba,Tace Bakomi,
Tace to Allah Yasa,
Tace Mata Ta Tashi ta koma Daki,Tana Zuwa Daki ta Zauna Sai ga Kiran Waccar Kawar ta ta da Suka Nufi Gidan Su Ita da Wancan Bawan Allah din,Tana Mai Ce Mata Lafia Naji Shiru Baku Iso ba Tun Ina Zaman Jiran Tsammanin Zuwan ku harna gaji,Sai Taji Tayi ajiyar Zuciya,Sai Kawar take Tambayar ta ko Lafia kuwa taji tana anjiyar Zuciya,????
Sai Tace Mata ai Sun Faasa Zuwa,Sai Tace Miyasa ???
Sai Take Gaya Mata Abinda Yafaru daga Alifun Har Ya'un,
Bata Iya Fadin komi ba Sai Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,
Takara da Laa Haula Wala Quwwata Illa Billahil Aliyyil Azeem,
Sai Taake Kawarta Da Zata Raka Saurayin Zuwa Wajen ta take Tambayar ta to Sai kikayi ya Dashi????Sai Take Ce Mata Nima Bansani Masa ba Tunda a Wurin na Barshi,Kuma Bakin Ciki da Takaici da daamuwar hakan Yahana In Sanar dake Halin da ake Ciki Jim kadan bayan Faruwar Al'amarin kafin In koma Gida,
Sai Kawar Tata tayi Mata Jaje Da Allah Ya kyauta Abinda Yafaru da'ita,
Ta amsa dakyau,ta Kuma ji dadi da jajen da tayi Mata,
Sai Ita Kawar take Tambayar ta aike Baki Ma Fadamin ko Waye Zaku Zo Wurina Tare Dashi ba Duk da kince Yace Ni friends Dinshi ce Yasan Ni Na San Shi,
Sai Tace Mata..........nee,Sai take Fada Mata Aida Tun Farko kingaya min Shine danace miki Kisan Yadda Zakiyi ki rabu Dashi bada Jimawa ba,Ni Kuma Ince Miki Bananan a Gida Natafi Garin su Umman mu,Haka Yaafi{Gari ne},Saboda Banson ji ko Ganin sa kwata~kwata
Sai Take Tambayar ta miyasa Zatayi hakan????Sai take ce Mata tasan Shi tasan Halin Shi,Suna Faara Chat Ko Sati Biyu basuyi ba Tagane Wannan Ba Mutumin kirki bane,Kuma Babu Qaruwa a Hiira Dashi Sai Bata Lokacin da Mutum Zaiyi Wanda Gaara Taya Yarinyar Kishiyar Uwa Wankin Kayan Maman su,
Sai Tace Mata to Allah ya kyauta,
Sai Ita Mai Saurayin ta Tambayi Waccar akan a Wanne Gari Yace Mata yake ???
Saita Fada Mata,Sai taji da Banbanci da yadda Yafada Mata,
To Sai Ita Wannan Mai Saurayin Ta Binciki Kawarta Wadda Suke Gari Daya da Wannan Saurayin,Sai Take Tambayar ta akan ko ta San Mai Wannan Sunan a Da'irar su,????
Sai takece Mata Yauma ita Tafara jin Sunan a Bakin ta,Tace Gaskiya da akwai Wani Mai Wannan Sunan a Tsakanin Yan Uwa da nasani,Saboda Bamuda Yawan da Zamu Rasa Sanin Junan mu,In Bakasan Sunan yaron ba za Kasan Sunan Mahaifin sa,
Tace Mata Gaskiya nee,Sai Mamaki yayi Mata Yawa,Taake ta Kira kawartan da Suke Gari Guda da Zata raka Saurayin Wurin ta, Tafada Mata ta Binciki Wata Sista a Garin dayace acan yake tace Wai batasan Shi ba,Yauma Tafara jin Sunan Shi a Bakin ta,
Ana Haka Sai Waccar Kawar da Za'a kaiwa Ziyara Itama ta Binciki Wata Sista a Garin Daya Fada Mata acan yake, Sai take Tambayar ta don Allah ko Tasan wani Dan Uwa Mai Wannan Sunan a Da'irar su,???
Sai Takece Mata Na'am Tasani,Sai tace Mata Wayeshi Kuma Da Gaske a Garin Nasu Yakeda Zama ??????
Sai Kawar ta ta Tace Mata Gaskiya Batasan Shi ba,Amma Tayi hakuri Zaata Bincika Mata,
Binciken da Tayi akan Wannan Saurayin ya Tabbata Cewa Ba Dan Asalin Garin Bane,Zuwa yake Yayi Raani in Lokacin Raani Yayi Sai Yatafi,Wani Lokacin ma akan yi Shekara Uku Hudu Bai Zo ba,Harsai Anfara Tunanin ko bazai Kara Zuwa ba Kawai Sai a Ganshi yadawo, Sannan a Binciken Aka Tabbatar Mata da Cewa ba Dan Uwa Almajirin Sayyeed Allama Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky {H} Bane,Bugu da Kari Duba da Take`taken sa an Hana Kowacce Sista Sauraren Shi a Gida ko a Hanya,Haka Shima Anja Masa kunne da Kashedin Zuwa Wurin Kowacce Sista a Fadin Da'irar da kewaye,Tare da Tsoratar Dashi Da Fuskantar Kakkausan Hukuncin Bijirewa Wannan Umarnin da'aka bashi Daga Harisawan Garin,
To daga Ranar Wata Sister Bata Qaara Tsayawa Dashi ba a Gida ko a Waje,Shima Kuma baikara Zuwa wurin Wata Sister ba tun daga Wannan ranar da'aka ja Masa kunne akayi Masa Kashedin,
#Free Sayyeed Allama Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky {H} His Wife and Followers.
Abdullahi Ibraheem Isah Dabai{Bawan Allah} +2347036969346
@Tacewa Da Yadawa Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
Labarin ya sosa min zuciya sosai
ReplyDelete