@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
من أقوال الإمام علي عليه السلام:
Cikin zantuka na hikima daga Imam Ali (A. S) yana cewa ;
" لا تقل ما لا تعلم ، بل لا تقل كلَّ ما تعلم ."
FASSARA
" KADA KA FADI ABINDA BA KA SANI BA, KAI, KADA MA KA FADI DUKKAN ABINDA KA SANI,?
SHARHI
---------------
Fadin abinda mutum bai sani ba yakan maida shi maqaryaci, domin zai fadi abinda yake cin karo da zantuka na gaskiya .
Sannan kawai don ka san abu sai kace za ka fade shi ba tare da an tambaye ka yakan shafi mutuncinka.
Wannan magana tayi daidai da fadin Ma'aiki (S. A. W. W) inda yake cewa;
" YANA DAGA CIKIN CIKAR MUSLIMCIN MUTUM BARIN ABINDA BAI SHAFE BA. "
Wato mutunci shine shiga cikin abinda aka so ayi da kai, amma duk wani abinda bai shafe ka sai ka kiyaye shiga cikinsa, sai dai in shirun naka zai sa a zalunci wani, ko kuma zai taimaka wajen cigaba da zaluntar wani.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
7th Sep, 2020/ 19th Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com