Bin Abinda Manzon Allah (S) Yazo Mana Dashi Na Qur'ani, Tare Da Riqo Da Iyalan Gidan Sa, Shine Mafitar Wannan Al'umma


Yan Kasata Najeriya, syn fara jin wahala, wahalar harta fara dawo musu da tunani mai kyau, ba cewa; "Komawa ga addinin Allah shine mafitar ko wannen dan Adam. Musamman a wannan kuncin rayuwa da yanayi da al'umma suke ciki.

To, bawai komawan bane, domin wannan kalamar ta komawa ansha nanata faden ta, amma ba'a dabbaqa ta, hasalima sai innan shiga kunci ne ake kawo ta a lissafi. Kaga kenen har yanzu da sauran rina a kaba.

Abin dai shine, dole ta zam munji kuma mun aminta a aikace da kuma furucin cewa; tabbas, addinin ne da gaske muke son yayi iko damu, ta hanyar gyara halayen mu, da komawa ga Allah wajen ibadu da kusantar gaskiya hadi da nemawa waɗanda ake zalumta yancin su.

Shi, addini aiki ne ba furuci kawai a baki ba, su dukan abu guda ne, furuci da aiki. Kai aikin ma shine al-muhum, amma muna kwance wai luna kiran a koma ga addini shine mafita, to wanne motsi kayi azzalumai har suka gane yanzu fa duniya ta juya musu baya, al'umma adalci kawai suke so?

Kullum ana zalumtar mutane a cikin gida da kasashen qetare, amma ba wanda yaje daga wa azzalumai dan yatsa bakke su firgita, suma su dawo hayyacin su din su gane, lokaci yayi da za'a cenza su da qarfin tsiya.

Su azzaluman nan kullum mune muke qara basu damar zalumtar yan uwan mu, sabida rashin dagewa da yi musu bara'a. Mutumin da yake zalumtar ka, amma kullum wai fata kake da a kansa, kana tunanin wani irin sa azzalumi wai shine mai adalci! 

Taya hakan zai samu, bacin duk uwa daya ce ta yaye su, ba'a basu mulki sai sun yarda zasu bi umurnin iyayen gidan su, malamai kuma sun dode kunnen su son kudi yayi musu yawa basa fitowa su fadawa mutane gaskiya, har tare dasu ma ake wa azzalumai 'Campaign'. To, gashi nan dai yanzu sai ku qara daukar darasi akan wannan Baban Naku Mai Gaskiya, wanda kansa kuke ta kafirta yan uwan ku Musulmai.

Allah ya sa mu dace, ya cenja mana wannan qunci da muke ciki, ya koma sauqi. Ya Allah ka fito mana da malamin mu (H), ka kuma bashi lafiya mai dorewa.

©Bin Haroun Sigau

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post