A ranar Litinin 31 ga watan August 2020 wannan mujallar mai suna Charlie Hedbo dake kasar Faransa mallalin Yahudawa ta sake batanci ga Manzon Allah (S), inda ta yi zanen wani hoto da suke buna cewa Manzo (S) ne dauke da Bom a kansa a matsayin rawani. Wannan zane da wannan la'ananniyar Mujalla tayi bashi bane karo na farko domin ta taba yin hakan a Shekarar 2015, Wanda haka ya haifar da rikici a lokacin.
A shekarar 2015 da suka yi wannan batanci wasu gungun matasan Musulmi ne dake kasar ta Faransa suka je har Ofishin mujallar suka kashe Shuwagabannin Ma'aikatar a matsayin sun dauki Fansa ga cin zarafin da ayiwa Annabinmu (S), Wanda yin hakan yasa Mujallar da hadin gwiwan Gwamnatin kasar ta Faransa suka ce zasu kara buga wani Cartoon din na Annabin Rahama (S), har wani mai matsayi a lokacin Wanda ake kira da Paparoma ya bayyana cewa lallai abin da Mujallar tayi bai dace ba, amma Farai Ministan Ingila ya fito ya bayyana cewa bai ji dadin maganar da Paparoma yayi ba.
Abin lura a nan shine bai kamata mu a matsayin mu na Al'ummar Annabi Muhammad (S) mu bari ana cigaba da batanci ga Manzon mu ba, wannan shine karo na biyu da suyi haka kuma lallai idan aka cigaba da barinsu wata rana abin da yafi haka ma zasu yi. Ya kamata mu farka, Marubutanmu, Yan Jaridanmu, Malamanmu, Matasanmu, Masu kare hakkin Musulmi na Duniya su shiga wannan lamarin. Mu fito mu bayyana Duniya cewa lallai bamu yarda da wannan cin zarafin da akeyi ga Manzon mu ba, wannan shine babban Jahadi.
Mu Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) muna Allah wadai da wannan Mujallar da duk masu goyon bayan ta. Allah ya rusata ya wulaqanta ma'aikatanta da duk masu hannu a wannan irin ayyuka nata. Kuma muna kira ga Al'umma dasu fito su bayyanawa Duniya rashin amincewarsu bisa wannan mummunan aiki, hakan zai sa wannan miyagun mutanen su gane lallai muna tare da Annabi mu kuma su kiyaye taba mutumcinsa. Allah yasa mu dace.
- 2/September/2020
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com