Baka Da Hujjar Qin Cin Abincin Da 'Dan Uwanka Musulmi Ya Yanka


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DA YAWA SUNA BATAR DA MUTANE NE BA BISA ILIMI BA 


Magama ce wacce babu wani musulmi da ke inkarin ma'anarta don a bayyane take yadda ba za a musanta ta ba. Allah (T) na cewa; 


" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KUCI DAGA (dabbobin da ) AKA AMBACI SUNAN ALLAH A KANTA IN KUN KASANCE MASU IMANI DA AYOYINSA ."


Sannan a shari'ar muslimci an bayyanar mana cewa idan mutum ya sami kansa a wajen sayar da abinci na musulmi to, ba shi da hujjar yin tambaya akan ya abin yake. 


Amma da shike 'yan Izala ba su da kunya kuma ba sunnah suke bi ba sai kaji suna cewa ba za suci nama ba saboda basu san wanda ya yanka ba. Amma kuma in ka sami kanka tare da su cikin wata seminar (workshop) ba sa yin irin wannan tambaya balle suqi cin naman da ke cikin abincin. 


Riwaya daga Hisham Bn Marwata, daga babansa, daga A'isha tace, aka ce;  


" Yaa Ma'aikin Allah ! Lalle anan akwai wasu mutane da ake bamu labarin cewa dayansu na yin shirka, kuma suna zo mana da nama amma bamu sani ba ko an yanka ko kuma a'a ." Yace; 


" TO, KU KU AMBACI SUNAN ALLAH A KANSA KUMA KUCI. "


(Bukhari, hadisi na 7398)


                 TAMBAYA 

                ------------------


Shin, dawa 'yan Izala ke yin koyi wajen ayyukansu da zantukansu? Domin naga ayyukansu na sabawa ne da umarnin Allah da Manzonsa (S. A. W. W) 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


 08126385470-08137925034


16th Sep, 2020/ 28th Muharram, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post