BAƘIN CIKI KASHE MAI YIN KA: Jinjina Ga Gwarzon Gwaraza jarimin Da Babu Irin Sa, Jarimi Kuma Jan gwarzo, Sheikh Dr. Ibraheem Yaqub Elzakzaky(H)


 


Kaine malami ɗaya tilo da ka gina almajiranka da haƙur da kuma ilimi, shi yasa ma babu jahili acikinsu. Kaine ɗaya tilo da Direban ka ma furefesa ne. 


Ba zance komi a ilimin addini ba saboda faɗi barnar baki (idan akwai jahili acikin almajiranka to malami ne acikin su) aɓangaren Ilimin zamani (Boko) kaikeda almajirai Dactoci da furofesoshi da masu Digiri ko HND kuma ka ginasu akan gudun duniya. 


Kaine ɗaya tal! Ƙwal! Da ya sadaukar da Rayuwarsa da dukiyar sa da ƴaƴansa gidan sa da motocinsa saboda Allah! Domin addinin Allah ya tabbata. 


Kaine ɗaya tilo da ya kafurcema ɗawagitai da tsarin kafurci kamar yanda annabawa da manzanni sukayi. 


Kaine mai mabiya sama da miliyan ashirin da suka yarda su bada rayuwarsu domin addinin Allah ya tabbata. 


Kaine wanda jami'a ta karrama da lambar girmamawa a matsayin DR bayan jawabin girmamawa daga shuwagabannin ta cewa 


Munbada wan'nan lambar ta ilimi ba dan tana daidai da kai ba, sai dan itace kawai lambar ilimi da mike da ikon bayarwa amma kawuce ta, da akwai wadda tafita da ita zamu baka. 

Tabbas wan'nan haka yake idan akayi duba da almajiranka. 


Sheda daga bakin wani almajirinka kuma farfesa yace :-Alokacin da muka ziyarci malam a gidan da suke tsare dashi muna labari dashi sai mukaji yana mana maganganu na ilimi da sanin halin da ƙasa take ciki kamar a waje yake muke tsare, yama fimu sanin halin da ƙasar take ciki. 


Wan'nan shedar daga bakin farfesa masani da ƙasa ke taƙama dashi. Don haka malamina ya wuce farfesa, amma muna jinjinama wan'nan jami'a da ta girmama malamin mu da iya abinda zata iya, kobakomi sun ƙara nunama jahilai da mahassada da maƙiya matsayin malam. 


Dafatan Allah ya ƙaramaka kariya da haƙuri Allah ya ƙara ɗaukaka darajarka, Allah ya fito mana da kai daga hannun azzalumai cikin izza da karama. 


Allah yayi amfani da mu mabiyanka domin ɗaukaka tutar la'ilaha illallahu muhammadurrasulillah (S) Allah ya cikamaka gurinka Allah ya farantamaka, muna murna kuma muna alfahari da wan'nan karramawa wanda zata fuskanci hujumi daga wajen maƙiya kwanan nan. Labbaika ya Elzakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post