A Bahrain an yi zanga zangar kin jinin sabudawar alakar da kasar ta kulla da Haramtaciyar Kasar Israila.An karfafa kwararen matakan tsaro yayin zanga zangar, sai dai duk da haka al’ummar kasar sun fito kan tituna domin nuna kin amincewarsu da kokarin da kasarsu ta ke yi na kulla alakar diplomasiyya da Haramtaciyar Kasar Israila.
Masu Zanga-zangar sun rika bayar da taken kin jinin ‘yan sahayoniya da kuma nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Palasdinu da kare hakkokin Palasdinawa.
A gefe daya shafukan sada zumunta na al’ummar kasar ta Bahrain, sun cika da taken yin tir da matakin na gwamnatin kasarsu na kulla hulda da ‘yan sahayoiya.
Har ila yau, wani daga cikin taken da aka rika bayarwa ya kunshi cewa; Babu yadda za a yi sulhu da ‘yan ta’adda.
Wani sashe na taken da masu Zanga-zangar su ka rika bayarwa ya kunshi cewa; Gwamnati ce ya kulla da ‘yan sahayoniya amma ba al’ummar Bahrain ba.
Source: Abna24.com
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
Tags:
Labaran Duniya