@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A RAGE YAWAN ROQO/BARACE-BARACE
kowanne dan Adam akwai yadda ya tarbiyyantar da zuciyarsa wanda hakan yasa take sarrafa shi yadda taso. Yadda ka bawa zuciyarka tarbiyya haka za ta tashi.
Na'am, a wani lokaci yanayi kan iya sa mutum yayi roqo, amma yinsa ba wata halitta bace wacce mutum zai ce haka Allah ya halicce shi da ita, a'a dabi'a ce wacce mutum ke yiwa zuciyarsa tarbiyya da ita.
Duk wanda ya bawa zuciyarsa irin wannan tarbiyya za ka same shi ba shi da kamun kai, babu godiya kuma babu wadatar zuci tare da shi ko da kuwa ya mallaki menene.
Yawan roqo na rage mutuncin mutum tare da cire kwarjini daga fuskarsa, kuma yakan cutar da wadanda ake yawan roqon su, domin akan takura su har abin yakai abinda ake kira QURE-HALI kamar yadda aka riqa yiwa Annabi (S. A. W. W).
Abu Sa'idil Khudriy ya kawo cewa, wasu mutane daga ansar (mutanen Madinah) sun roqi Manzon Allah (S. A. W. W) kuma babu wanda ya roqe shi daga cikinsu face ya ba shi, har takai abinda ke hannunsa ya qare. Yayin da komai na imfaqin da ke hannunsa ya qare sai yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" BABU WANI ABU NA ALKHAIRI (dana boye a hannuna ko a gida) WANDA BAN BA KU BA. LALLE SHI WANDA YA KAME KAI (daga cikinku) ALLAH ZAI BA SHI KAMUN KAI, KUMA WANDA YAYI HAQURI (bisa halin da yake ciki) ALLAH ZAI SANYA MAR HAQURI, KUMA WANDA YA WADATU ALLAH ZAI WADATA SHI. BABU WANI ABIN BAYARWA (kyauta daga Allah) WACCE ZA A BAWA MUTUM MAFI ALKHAIRI KUMA MAFI YALWA FIYE DA HAQURI. "
(Bukhari, hadisi na 6470)
Amma wani abin takaici sai kaga har wadanda ke kiran kansu malamai ko ake kiransu sun zama mabarata.
Wannan dalili yasa ba su da izzah wajen azzaluman mahukunta, kuma ba su da qima wajen mabiyansu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
13th Sep, 2020/ 25th Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com