@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DAGA WA'AZOZIN ABU ZARR AL-GIFARIY
Abu Zarr (R. A) yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
قال أبو ذر رضي الله عنه: هل ترى الناس ما أكثرهم؟ ما فيهم خير، إلا تقي أو تائب.
FASSARA
-----------------
" SHIN, KANA GANIN MUTANE DA ABINDA YA YAWAITA SU ? BABU WANI ALKHAIRI CIKINSU FACE WANDA KE JIN TSORON ALLAH KO KUMA WANDA KE TUBA ."
(Mawa'izatul-Sahabah)
SHARHI
--------------
Ganin taron jama'ah da yawansu ba komai bane wanda zai ba ka sha'awa matuqar babu tsoron Allah cikinsu kuma suna sabawa Allah ba tare da suna tuba ba.
Shi yasa ma Allah ke mana nuni don mu sani cewa mafi yawan mutane basu da hankali ko ilimi ko kuma fahintar gaskiya.
Tsoron Allah da tuba gare shi shine alkhairin da ke cikin mutane, Idan aka rasa wannan babu alkhairi cikinsu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
21st Sep, 2020/ 4th Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com