@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Imam Sadiq (A. S) ya nusar damu kan abubuwa biyar wadanda sune ke nuna cewa mutum kammalalle ne, matuqar ya rasa su to tamkar dabba yake ko da kuwa yana magana ana sauraronsa.
Ga su cikin hadisi kamar haka;
👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽
ل، الخصال أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ يَزِيدَ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ قُتَيْبَةَ الْبَصْرِيِّ عَنْ أَبِي خَالِدٍ الْعَجَمِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ:
" خَمْسٌ مَنْ لَمْ يَكُنَّ فِيهِ لَمْ يَكُنْ فِيهِ كَثِيرُ
مُسْتَمْتَعٍ الدِّينُ وَ الْعَقْلُ وَ الْأَدَبُ وَ الْحُرِّيَّةُ وَ حُسْنُ
الْخُلُقِ."
FASSARA
------------------
" ABUBUWA BIYAR WANDA YA RASA SU YA RASA ABUBUWA MASU YAWA NA JIN DADI.
(1)- ADDINI
(2)- HANKALI
(3)- LADABI
(4)- 'YANCI
(5)- KYAWAWAN 'DABI'U ."
(Biharul-Anwar, J:1, SH :83)
Wadannan abubuwa sun zama wajibi ga mutum ace yana tare dasu don inganta rayuwarsa ta duniya da lahira.
Duk wanda ya tattara wadannan abubuwa ya more rayuwarsa, domin dasu ake neman kusaci ga Allah. Kuma wadannan abubuwa ne mafi yawan mutane suka rasa, masamman malamai da mahukunta wannan qasa.
Mabiya mazhabar Ahlul-Bait (A. S) 'yan shi'ah ne kadai ke da wannan siffa in ka cire abu guda 1 ('yanci) wanda azzalumar hukuma ta hana musu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
9th Sep, 2020/ 21st Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com