@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Alqaqarin Allah ne cewa ba zai damqa al'amarin Imamanci a hannun azzalumi ba, amma yakan bada mulki ga fajiri, ja'iri ko azzalumi.
Duk wanda kaga ya yi mulki da sunan muslimci ba Hakan na nuna cewa shi adali bane, sannan ba hakan na nuna cewa Allah ya yarda da mulkin nasa bane.
Ya zo cikin Tafsirin Qummi cewa;
- فس، تفسير القمي لَمَّا عَزَمَ إِبْرَاهِيمُ عَلَى ذَبْحِ ابْنِهِ وَ سَلَّمَا لِأَمْرِ اللَّهِ قَالَ اللَّهُ
Yayin da Ibrahim (A. S) yayi azamar yanka dansa Isma'il (A. S) kuma ya sallama don al'amarin Allah sai Allah yace,
إِنِّي جاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِماماً
" LALLE NI MAI SANYA KA IMAMI (jagora) NE GA MUTANE ."
فَقَالَ إِبْرَاهِيمُ ع وَ مِنْ ذُرِّيَّتِي
Sai Ibrahim (A. S) yace ; " KUMA (ka sanya wannan imamancin) DAGA ZURIYATA ." Sai Allah yace;
قالَ لا يَنالُ عَهْدِي الظَّالِمِينَ
" ALQAWARINA (na wannan imamancin) BA YA SAMUN AZZALUMAI ."
أَيْ لَا يَكُونُ بِعَهْدِي إِمَامٌ ظَالِمٌ[17].
Abin nufi alqawarina ne cewa Imamanci ba ya samun azzalumai.
__________________________
(1) تفسير القمّيّ: 50. م.
(7) تفسير الإمام: 212، الاحتجاج: 18 و الرواية مفصلة فيه. م
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج12، ص: 61
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
24th Sep, 2020/ 7th Muharram, 1442
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com