@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
من أقوال الإمام علي عليه السلام:
Ko ba bisa Shari'a ba, yawan magana kan rage mutuncin mutum. Duk inda ka sami mai yawan surutu za ka tarar yana da qarya cikin zantukansa.
Masu irin wannan dabi'a so suke su zama su kadai ake jin su yayin zamansu cikin jama'ah. Saboda haka sai ya riqa yin qarya don a gaskata shi.
To, ga abinda Imam Ali (A. S) ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" إذا تمَّ العقل نقص الكلام ."
FASSARA
-------------------
" IDAN HANKALI YA CIKA (ga mutum) MAGANA KAN RAGU (gare shi ) ."
Ba za ka taba samun mai cikakken hankali na yawan magana cikin jama'ah ba.
Hakan na nuna mana ana iya gane mai cikakken hankali ta wajen qaranta magana in ba buqatar maganar ne ya kama ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08138925034
19th Sep, 2020/ 2nd Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com