AUREN IMAM ALI DA SAYYIDAH FATIMA: Na Amince Da Wannan Auren Yaa Ma'aikin Allah (s.a.w.w)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Ya zo cikin riwayoyi mabambanta amma masu ma'ana iri daya dangane da auren Imam Ali (A. S) da Sayyidah Fatima (S. A) cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 أَنَّ النِّسْوَةَ قُلْنَ يَا بِنْتَ رَسُولِ اللَّهِ خَطَبَكِ فُلَانٌ وَ فُلَانٌ فَرَدَّهُمْ أَبُوكِ وَ زَوَّجَكِ عَائِلًا فَدَخَلَ رَسُولُ اللَّهِ ص فَقَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ زَوَّجْتَنِي عَائِلًا فَهَزَّ رَسُولُ اللَّهِ ص بِيَدِهِ مِعْصَمَهَا وَ قَالَ لَا يَا فَاطِمَةُ وَ لَكِنْ زَوَّجْتُكِ أَقْدَمَهُمْ سِلْماً وَ أَكْثَرَهُمْ عِلْماً وَ أَعْظَمَهُمْ حِلْماً أَ مَا عَلِمْتِ يَا فَاطِمَةُ أَنَّهُ أَخِي فِي الدُّنْيَا وَ الْآخِرَةِ فَضَحِكَتْ وَ قَالَتْ رَضِيتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ.


Lalle mata suka ce, yaa 'yar Ma'aikin Allah ! Wane da wane sun nemi auren ki amma sai babanki ya mayar dasu ya aura miki talaka. Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya shigo sai tace masa;


" Yaa Ma'aikin Allah ! Ka aura min talaka (kamar yadda matan ke cewa) ." Sai (S. A. W. W) ya riqa karkada dan yatsansa yana nuna ta da shi yace; 


" A'A YA FADIMATU ! SAI DAI NI NA AURA MIKI WANDA YA RIGAYE SU A MUSLIMCI , KUMA WANDA YA FISU YAWAN ILIMI, KUMA MAFI GIRMANSU A HAQURI. AMMA KIN SANI KUWA YAA FADIMATU CEWA SHI 'DAN'UWANA NE A DUNIYA DA LAHIRA ?


Sai tayi murmushi ☺ tace; 


" NA AMINCE (da wannan zabin naka) YAA MA'AIKIN ALLAH ."


وَ فِي رِوَايَةِ أَبِي قُبَيْلٍ‏ لَمْ أُزَوِّجْكِ حَتَّى أَمَرَنِي جَبْرَئِيلُ.


A riwayar baban Qubail yace; 


" BAN AURAR MIKI BA HAR SAIDA JIBRILU (A. S) YA UMARCE NI ."


وَ فِي رِوَايَةِ عِمْرَانَ بْنِ الْحُصَيْنِ وَ حَبِيبِ بْنِ أَبِي ثَابِتٍ‏ أَمَا إِنِّي قَدْ زَوَّجْتُكِ خَيْرَ مَنْ أَعْلَمُ.


A riwayar Imrana Bn Husain da Habeeb Bn Thaabit Abiy ,


" AMMA NI DAI NA AURA MIKI MAFI ALKHAIRIN WANDA NA SANI (cikin Sahabbaina) .


وَ فِي رِوَايَةِ ابْنِ غَسَّانَ‏ زَوَّجْتُكِ خَيْرَهُمْ.


A riwayar Ibn Gassan, 


" NA AURA MIKI MAFI ALKHAIRINSU NE !"


وَ فِي كِتَابِ ابْنِ شَاهِينَ عَبْدِ الرَّزَّاقِ عَنْ مُعَمَّرٍ عَنْ أَيُّوبَ عَنْ عِكْرِمَةَ قَالَ النَّبِيُّ ص‏ أَنْكَحْتُكِ أَحَبَّ أَهْلِي إِلَيَ‏


A cikin littafin Ibn Haasheen Abdurrazaq , daga Mu'ammar , daga Ayuba daga Ikrimata cewa, Annabi (S. A. W. W) yace, 


" NA AURA MIKI MAFI SOYUWA NE GARE NI CIKIN IYALINA ."


__________________________


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 150


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        (08126385470)


27th Sep, 2020/ 10th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post