Musa Hasan Shinkafi a Bangaren Dama Sai Mas'udu Dan Masani Shinkafi a Bangaren hagu |
Sunana Musa Hassan Shinkafi,
A Matsayina na Musulmi Almajirin Sheikh Ibrahim Zakzaky (h), Kuma daya daga Cikin Dubban Matasa Almajiran Sheikh Zakzaky Masu Bibiyar Shirye Shiryen Hausa Movies da akafi Sani da Kannywood.
Bamuji dadin yadda Muka ga Fuskar Daya daga Cikin Jaruman Masana'atar ku Mai suna Yakubu Mohammad, ta fito a Cikin Wani Shirin film da ake kokarin Bata Sunan Musulmi Almajirin Sheikh Ibrahim Zakzaky Wanda ake Shiryawa a Jahar Enugu Dake Kudancin Najeriya Mai suna "Fatal Arrogance"
Muna kiran ga Shugabannin Kannywood kuyi gaggawar Daukar Matakin bincike Kuma ku dauki mataki akan Wannan Matsala.
Film din "Fatal Arrogance" dai tuni bincike Ya gama tabbatar da cewa Rundunar Sojojin Najeriya ce ta dauki nauyin Shirya Film din, Domin Canzawa Al'umma Najeriya tunani da Jefa Shakku a Zukatansu akan Yadda Suke kallon Da'awar Sheikh Ibrahim Zakzaky da kyakyawan tsari da Manufa Mai kyau Zuwa Wani Abu Mai kama da na Ta'addaci.
Kuma Wannan Yana daga cikin kokarin Sojojin Najeriya na Rufe gaskiyar Kisan kiyashi da Sukayi a Zariya 12/12/ 2015.
Idan Har Masa'antar Kannywood ta kasa Fitowa ta Fada Mana Matsayin ta akan Rashin adalci da Kokarin batawa Sheikh Ibrahim Zakzaky da Almjiransa Suna da daya daga cikin Jarumai a Masana'anta yayi to lallai Zamu dauki Matakin yiwa kamfanin tawaye ta hanyar kauracewa kallon Shirye Shirye ku.