✍️Auwal M. Tukur
10 September,2020
Kira na ga 'yan uwa almajran Malam Zakzaky kan wannan film din da aka bayar da kwangilarsa ga 'yan film na Kudu. To dama shi dai wannan tsararren abu ne daga gwamnatin tarayya.
Abinda muka lura da shi, shi ne, a ita gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Buhari a kokarinta na ci gaba da aikin kwangilar da ta karbo daga kasar Saudiyya na batawa Malam Zakzaky suna da Harkar Musulunci da yakewa jagoranci, shi ne sunga sa karfin bindiga ba zai sa su cinma hadafinsu ba, shi yasa suka fara tunanin amfani da wasu kafafe kamar rubuta littafi, tsara film d.s.
A wani dan kwarya-kwaryar bincike da na gudanar dangane da wannan film din shi ne zan yi bayani yanzu.
Wannan film din a binciken da nayi, ya samo asali ne tun ranar 20 ga watan Fabairu na wannan shekarar ta 2020. Inda wata babbar Makaratar (Higher Institution) mai suna, "Centre for International and Strategic Studies" wacce Prof. Ahmad Danfulani yake Jagoranta. Wanda bayan Wannan prof. Din a kwai wasu da dama na daga cikin wannan gwamnatin da sune iyayen taron. Kamar gwamnan jihar Benue Samuel Ortom wanda shi ne Babban bako a wurin. Sai kuma wanda ya wallafa wannan littafin Terrence Kuanum. Inda a ciki, bayanan da sukayi a kan wannan littafin da suka wallafa mai suna _Fatal Arrogance_ suyin kage da danganta Harka Musulunci da kungiyar ta'addanci.
To kusan wannan littafin ta nan ne har suka samu damar mayar da shi film.
Tunda sun lura yanzu film ya fi tasiri da saurin isar da sako. Shi ne yasa suka mayar da littafin film, kuma suka yi amfani da sunan littafin ga film din.
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com