@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IN KO YA TABBATA HAKA BA ZAI TABA ZAMA ABIN KOYI BA
Allah (T) da kansa ya shaidi Manzonsa (S. A. W. W) da aikata kyawawan dabi'u, har ma yayi mana umarni cewa muyi koyi da shi (S. A. W. W) cikin komai nasa.
Yana daga cikin kyawawan dabi'u aikata abinda mutum ke fada, ma'ana ya kasance yana aikata abinda yake umartar mutane da shi, ko kuma barin abinda yayi hani a kansa.
Fadin abinda mutum ba ya aikatawa abin zargi ne, shi yasa Allah (T) yayi zargi kan haka.
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! DON ME KUKE FADIN ABINDA BA KWA AIKATAWA? YA GIRMA YA ZAMA ABIN QYAMA WAJEN ALLAH KU RIQA FADIN ABINDA BA KWA AIKATAWA ."
(suratul-Saff, aya ta 2-3)
KALLON ALQIBLA KO JUYA MATA BAYA YAYIN BIYAN BUQATA
Riwayoyi biyu (2) masu cin karo da juna sun zo cikin Bukhari kamar haka;
(1)- Abu Ayuba Al-Ansari yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" IDAN 'DAYANKU YA JEWA BIYAN BUQATA (gha'idi), TO, KADA YA FUSKANCI ALQIBLA KUMA KADA YA JUYA MATA BAYA, YA KAIKATA (kudu/arewa) ."
(Bukhari, hadisi na 144)
(2)- Riwayar Ibn Umar kuma yace;
" NA HAU KAN RUFIN GIDAN HAFSAT (matar Annabi) DON BIYAN WATA BUQATA, SAI NAGA MANZON ALLAH (S) YANA BIYAN BUQATARSA YA JUYAWA ALQIBLA BAYA YANA KALLON SHAM ."
(Bukhari, hadisi na 148)
NAZARI
Cikin hadisi na farko za muga cewa Annabi (S. A. W. W) yana mana hani ne game da kallon alqibla ko juya mata baya, amma cikin hadisi na biyu kuma yana nuni ne cewa Annabi na aikata abinda yake yin hani a kansa.
Anya wannan magana tayi kama da gaskiya kuwa? Sannan kuma ladabi ne ace mutum yaga mahaifinsa na biyan buqata irin ta 'yan adamtaka sannan yazo yana bada labari?
Amma dai ku tayani nazari cikin maganar Ibn Umar, domin yana nuna mana ne cewa abinda Annabi (S. A. W. W) ke fada dabam abinda yake aikatawa ma dabam. Kuma ba ladabi bane a riqa leqen Annabi (S) yayin biyan buqata sannan azo ana bada labari don neman
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com