Area Commander na yankin kontagora jihar Niger Yana kokarin tada wata rigima tsakaninsa da yan'uwa musulmi.



Yan'uwa musulmi almajiran sheikh Ibrahim zakzaky (H) na garin kamfanin Bobi sun fito rana alhamis kamar yanda sauran al'umar Muslimi suka fito a ranar ashura Dan su taya manzon Allah jaje akan kisan dansa Imam Hussaini a goma ga watan Muharram Amma Area Commander ya tura jami'an tsaro suka Kama yan'uwa na garin kamfanin Bobi tare da tsaresu tsawon kwanaki hudu ba tare da miqasu kotu ba. Wanda hakan ya Saba kundin tsarin kasa aje mutum sama da awa 24. Hakan yasa Area Commander ya Hana yan'uwa ganawa da wadanda suka Kama. Kuma sun hana su abinci tin ranar alhamis har ranar Asabar. Sai dai anyi ta kokarin samu a gana shi Area commander. Abin ya cutura, idan wani daga cikin yan sandan mai suna Yusuf Akande. Ya yake gayawa yan uwa cewa Area commander, ya tafi hutu, da Kuma cewa Gwamna ya zo suna cen tare da shi dai sai sauran maganganu. Wanda da har zuwa yau ba su Bari an gana da yan uwanda suka Kama ba. Tin ranar Laraba 9/9/2020 suna tsare da su. Kwatsam Sai gashi yau 14/9/2020 aka kai su kotu. Cewa suna tuhumar Yan uwan da laifin wai sun fito sunyi muzahara. Bayan gwamnati ta soke Shi'a da Kuma tarukan Shi'a a Nigeria.


Sai dai abinda majiyar mu ta tabbatar mana shine, Area commander dama cen, yana da ra'ayin Yan Kungiya ne. Dan haka yanzu yana kokarin samun kafar yin abinda ya dade yana jira. Duk da cewa tin a sauran muzaharorin da ake yi annan cikin garin Kontagora, sukan yi iya kokarin na ganin sun kawo wani abu na tashin hankali domin shafawa harka kashin kaji. In ya zuwa hada wannan rahoton, mun samu tabbacin cewa alkalin ya iso kotun domin fara shari'ar. Wannan shine halinda ake ciki. 

Dan haka muna baran addu'arku yan'uwa.


___Auwal M Tukur

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post