Daga : Isma'il Abubakar Idris Katsina.
Wani babban Limamin Masallacin Juma'a na Oando da ke garin Abuja a unguwar Katamfe bayan kammala Firi huduba Limamain yayi kiya ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari akan ya Sassautama Talakawa akan kunci da tsadar rayuwarda ya sanyaso da halin kaka nikayi.
Limamin dai fara da cewa " ada munyi shiru da Shugaban kasa ya kara kudin man fetir Lita 145 amma yanzu bazamuyi shiru ba akan yadda ya maida Litar man Fetir 160, muna zaton Wuta a Makera sai ta billa a masaka, muna zaton karinda Shugaban Kasa yayi na farko akwai manufar da yake nufi ashe manufarshi sanya talakawa halin kaka nakayu".
Limamin ya kara da cewa " Buhari idan na tare dakai basu fadima gaskiya mu zamu fadima koda zamuyi ta bakin ranmu, Talakawa sun shiga kuncun rayuwa shinkafa ta gagari Talaka, Masara sai mai Kudi, Buhari ka bada Umurnin a fitar da Tan 30 na Masara domin masu kiwan Kaji tomu Talakawafa.....?".
Buhari idan kaje lahira zaka amso tambayoyi akan kowane Talakan kasar ka, Zalunci baya dorewa ya kamata kaji da Halinda ka jefa Talakawan Najeriya na rishin tsaro anata kashe mutane ba gaira ba sabar, ga Kidnappen ya addabi Hanyoyinmu, an dauki rayukan Talakawa ba'a bakin komi ba!, Buhari kaji tsoron Allah
Daga karshe Limamin ya kara da cewa " Buhari gara ka maida Kasarmu a yadda take a baya fiye da yadda muke a yanzu, karshe limamin ya bukaci dukkan wani mai hanyar sadarwa ta yadda abin da ya fada zai kai ga wani Babba ko wani kusa maifada aji a Najeriya ko zuwa ga shugaban Kasa mutum ya Wallafa.
Malamin yayi addu'a an kira Sallah lokaci yayi.
Jama'a ku tayani yadawa, Naku Isma'il Abubakar Idris Katsina, Mai-tama Abuja
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com