An Kama Mayakan ‘Yan Ta’adda Na Kungiyar Daesh 12 A Lardin Ambar Na Kasar Iraqi

Ma’aikatar ‘yansandan ciki, na kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa jami’an tsaron kasar sun kama mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh su 12 a Lardin Ambar na yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran ABNA24 na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar ta Iraqi ta na fadar haka a jiya Litanin, ta kuma kara da cewa:

“Wadanda aka kama, sun arce daga kasar ta Iraqi zawa wata kasa makobciyar kasar, bayan da jami’an tsaron kasar suka kwaci iko da Lardin a shekara ta 2017, amma suka sake dawowa don aiwatar da ayyukan ta’addanci”.

Labarin ya kara da cewa jami’an tsaro a lardin na Ambar sun gano rumbun ajiyar makamai da kayakin aikin soja, na mayakan, wadanda suka hada da, manya-manyan bindigogi, damarar kunan bakin wake, makamai masu linzami samfurin katusha, makamin harba rokoki da kayakin aikin soja da dama.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post