@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
من أقوال الإمام علي عليه السلام:
Ya zo cikin zantukansa na hikima (A. S) yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" شيئان لا يوزن ثوابهما العفو والعدل ."
" ABUBUWA BIYU SAKAMAKONSU BA ZAI AUNU BA, YAFIYA DA KUMA ADALCI ."
Cikin wannan zance na Imam Ali (A. S) wanda ke cike da hikima yana nuna mana ne girman lada ko sakamakon abubuwa biyun nan masu wuyar kiyayewa wajen mafi yawan mutane.
(1)-YAFIYA :- Allah (T) ya yi umarni da yin yafiya inda yake cewa;
" KUYI YAFIYA KUMA KU KAUDA KAI (daga mummunan abinda akayi muku) , SHIN KO BA KWA SON ALLAH YA GAFARTA MUKU NE ?"
Da yawa mutane sun gaza yin yafiya ga 'yan'uwanau yayin da aka manana musu.
(2)- ADALCI :- Yin adalci shi yafi daidaita komai a rayuwa kuma mafi yawan mutane sun rasa shi tare da su. Allah (T) kuwa na cewa;
" KUYI ADALCI SHINE MAFI KUSACI DA TAQWA ."
Saboda haka ladan wadannan abubuwa biyu ba za su taba aunuwa a girman lada ba .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
17th Muharram, 1442/ 29th Sep, 2020