MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES
Bayan kisan ta'addanci na qare dangi da akayi ga iyalan Ma'aiki (S) a filin Karbala, sai Ibn Ziyad (L A) ya tattara sauran qananan yara da mata da kuma Imam Aliyu Zainul-Abideen (A S) marar lafiya ya tura su zuwa Sham Fadar Yazid (L A).
Zajr Bn Qais shine ya jagorance su su kayi wannan tafiya a qasa ba takalma, ba hutawa, kuma a tantanke cikin Mari (Sarqa), yayin da shi kuma ke haye kan Doki.
.
Da aka iso fadar Yazid (L A) da wadannan tsarkakan Bayin Allah, kuma aka nuna masa kan Imam Hussaini (A S) tsire kan tsinin Mashi, sai yayi farin ciki har ya dau Kwagiri yana wasa da dashi cikin wushiryar Imam Hussaini (A.S).
Abu Burdatal-Aslamiy (R.A) na zaune a garin, ganin abinda Yazid ke yi da kan Imam Hussaini sai yace;
" Yanzu wasa kake da Kwagirinka cikin wushiryarsa? Amma haqiqa ni naga Manzon Allah (S) yana sumbatarsa (kiss). Yanzu kai Yazidu ka aminta Ibn Ziyad yazo a matsayin mai cetonka ranar alqiyama, kuma wannan (Hussaini) yazo Muhammad (S) ya zama mai ceto gare shi ?"
Sai Yazid (L.A) ya miqe daga gurin da yake zaune yace;
" WALLAHI DA NINE NAKE TARE DA SHI (a Karbala ) DA BAN KASHE SHI BA ."
Sannan yace;
" AMMA SHIN KA SAN WANNAN 'DIN DAGA INA YAKE? KUMA MA ABINDA YAKE CEWA SHINE; " Ubana yafi Ubansa alkhairi, kuma Uwata Fadimatu tafi Uwarsa alkhairi, kuma kakana Manzon Allah (S) yafi kakansa alkhairi, sannan ni nafi Yazidu alkhairi, kuma ni nafi cancanta da wannan al'amari ba shi ba ."
" TO, FADINSA CEWA UBANSA YA FI UBANA ALKHAIRI, HAQIQA UBANA DA UBANSA ZA SUYI JAYAYYA GABAN ALLAH, KUMA MUTANE ZA SU SAN WA ZA AYI HUKUNCI A KANSA. AMMA FADINSA CEWA UWATA TA FI UWARSA, GASKIYAR AL'AMARI SHINE, FADIMATU 'YAR MANZON ALLAH (S) TA FI UWATA ALKHAIRI. SANNAN FADINSA CEWA KAKANA YA FI KAKANSA ALKHAIRI, TABBAS BABU WANDA YAYI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA ACE YANA GANIN MANZON ALLAH (S) DAIDAI YAKE DA WANINSA KO KUMA KISHIYARSA BA "
Zamuci Gaba insha Allah
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com