Zarif: HIK Ce Babbar Barazanar Nukiliya A Duniya

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya fada a jiya Laraba cewa; HKI ce barazanar Nukiliya ta farko a duniya, haka nan kuma a fagen keta hakkin dan’adam da mamaya.

Da yake Magana dangane da kin amincewar kasar Sudan na kulla alaka da HKI a wannan lokacin, minstan harkokin wajen Iran ya kara da cewa; Ta bakin Pempeo mun fahimci dalilin da ya sa Amurka take cire kasashe daga jerin wadanda take kira ‘yan ta’adda, shi ne kulla alaka da HKI.


Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa; “ Haramtacciyar Kasar Isra’ila ce babbar barazanar Nukiliya a duniya, kuma wacce take kan gaba wajen take hakkin dan’adam, sannan kuma ‘yar mamaya, bugu da kari ‘yar ta’adda, to ta yaya za a yi duniya ta dauki siyasar wajen Amurka da muhimmanci?

Ministan harkokin wajen Amurka ya ziyarci Palasdinu da take karkashin mamaya, daga can kuma ya nufi kasar Sudan domin yi wa kasar matsin lambata kulla alaka da ‘yan sahayoniya.

Fira ministan kasar ta Sudan ya bayyana cewa ganawarsa da Pempeo ta mayar da hankali ne akan yadda za a cire sunan kasar daga jerin ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; Abdullahi Hamduk ya fadawa ministan harkokin wajen na Amurka cewa; Bas shi da izinin kulla alaka da HKI.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post