ZARATAN YAN KWALLO A JIHAR KATSINA ZASU HAURA KASASHEN TURAI

Senator Malam Bello Mandiya zai tallafa wajen fitar da yan-kwallo Qafa dake Katsina ta Kudu zuwa Qasar Russia,

Alhaji Mustapha Yusuf Maigoro Tingilin Malumfashi shine ya kawo wannan cigaba a karkashin Kungiyar Kwallon Kafa ta Duniya mai Suna FDC VISTA,

Sai masu taimakawa wajen ganin wannan abun Alkhairi ya tabbata:-

Yan kwamitin sune

Chiyaman: Alhaji Ibrahim Dan-Juma

Ko'odineta: Auwal salisu Abdullahi kano

Sakatare: Kabiru Falalu

Malam Nasiru Ahmed (Bami)( Shuwagaban Kungiyar Alakalan Wasa na jahar Katsina)

Idris Babanta Funtua

Malam Abdullahi Mlf L.g Welfare Officer,

Mohammed Garba MG S.A Funtua zone,

Engr.Dr. Tukur Hassan Tingilin,

Adamu Ibrahim Alow(Shugaban Kungiyar Alakalan Wasa na Malumfashi)

Sai wakilan Shuwagabanni Kungiyoyin Kwallon Kafa dake kowacce karamar hukuma dake Kudancin Katsina,

Yadda fidda yan-Wasan zai kasance shine :-

 An sanya Kofi ne wanda za'a bukaci kowacce Karamar hukuma dake Kudancin Katsina su zabu Yanwasa mafi kyau a karamar hukumar Su domin fidda Ingantance Club na yan-Asalin karamar hukumar guda Biyu.

Kananun hukumomi 11 zasu buga wasan kwallon Kafar a stadiums din Malumfashi da Funtua da haka za'a fidda na Daya zuwa na Ukku wadanda za'aba kyaututtuka,

A Lokacin buga wasa dake kowacce karamar hukuma anan ne masu dubawa zasu duba yan-Wasan da suka cancanta a dauka, sannan zasu ba yaran da suka dauka scholarship suyi karatun digiri.

Saboda haka ba cin Gasar Kofin bane mafi abun kula ga yan-wasan,

Dan-Wasa ya Maida hankali wajen tsare Position din Shi saboda Kungiyar Kwallon Garin Ku na iya zuwa ta Qarshe wani cikin yan-wasanta ya zama na Daya wajen dauka,

ALLAH yasa gudanar da wannan Wasa lafiya yaba masu rabo Sa'a,

ALLAH kara wadata Mu da shuwagabanni Nagari,

  Amiin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post