Muzaharar Ashura: An Raunata Mutum Hudu A Kaduna
Jami'an tsaron Nijeriya sun afkawa 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) masu muzaharar #Ashura1442 a garin Kaduna a halin yanzu.
Ya zuwa karfe 3 da mintoci 12 na yammacin yau Lahadi, sun harbi 'yan'uwa akalla mutum hudu wadanda aka iya tantancewa a yanzu. A yayin da daya daga cikinsu kamar yadda majiyarmu ta tabbatar an harbe shi a kai ne.
Sai dai masu muzaharar duk da ruwan harsasai masu rai a kawukansu, sun samu sun karasa Junction na Leventis inda suka rufe Muzaharar sannan aka sallami 'yan'uwa kowa ya fara watsewa.
Tags:
MUNASABAR ASHURA