MA'ASUMAH ANGERIN NEWS UPDATE
Tare da wakilinmu Bashir Adam
(Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai)
Sallar gawa atsaye a keyi sannan tanada kabbarori guda biyar (5).
(1) idan anyi kabbarar farko sai Kalmar shahada.
(2) Kabbara tabiyu kuma ayi salati ga annabi Muhammad (s.a.w.w) da iyalan gidansa.
(3) Ta uku sai ayi addu'a ga muminai maza da mata.
4) Ta hudu sai ayi addu'a gashi mamacin na neman gafara da rahmar Allah agareshi.
(5) Ta biyar kuma sai sallamewa.
Sallar gawa sallace wanda ba'amata ruku'u bare sujada, kuma koda anbisne mamaci kafin ayi masa sallah saboda wasu dalilai, toh ana iya tsayawa akan kabarin ayi masa.
Ba'a la'akari da tsarkin jiki kona tufafi a sallar gawa, kuma duk wasu sharuddodi na sallar wajibi ba'a la'akari dasu.
A Sallar jana'iza, illa dai kawai ba'ason kyalkyacewa da dariya, koyin magana ayayin sallar. Duk da haka an so kula dasu a babin (istihbabi).
(ZUBDATUL- AHKAM) Allah yabamu ikon aikatawa. Ilahee.
SAHANNU
Barrister Nuraddeen isma'eel
Tags:
Makaranta