W.H.O: Cutar Corona Ba Ta Da Maganin Da Zai Zama“Sha Yanzu Magani Yanzu”



Hukumar lafiya ta duniya ta ja hankali a yau Litinin cewa; Ba Za a iya samun maganin da zai kawo karshen cutar corona cikin gaggawa.

Gargadin na kungiyar lafiya ta duniya ya zo ne a daidai lokacin da ke tsammanin samun allurar riga kafi ta maganin cutar ta lumfashi covid-19.

Shugaban kungiyar ta Lafiya ta duniya; Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa; Babu wani magani sha yanzu, magani yanzu dangane da cutar corona, watakila ma ba za a taba samun irin wannan maganin ba.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da cewa adadin mutanen da cutar ta harba a duniya sun haura miliyan 18, kuma tana ci gaba da yaduwa ta yadda a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata ta sake harbin mutane miliyan daya, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto.

Jaridar Washington Post ta nakalto wani masanin cutuka masu yaduwa a kasar Amurka daga jami’ar Havard yana cewa; Samar da allurar riga-kafi, masomi ne ka kawo karshen corona-ba shi ne karshe ba, domin ko an samar da maganin to yana da matakai da yake dauka na rarraba shi a duniya, zuwa kuma gaskata shi da mutane za su yi, wanda shi kanshi zai dauki watanni.

Har ila ya, masana sun bayyana cewa; Ba da an yi wa mutum allurar riga-kafi ba ne jikinsa yake samun garkuwa, hakan yada daukar makwanni.

SOURCE: ABNA24.COM

DUBA SABBIN LABARAI ANAN: http://www.maasumah.com.ng

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYOMUA SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN: @EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post