​Wata ‘Yar Sanda A UAE Ta Yi Murabus Saboda Kasar Ta Kulla Alaka Da Isra’ila

Daya daga cikin ‘yan sandan birnin Dubai na kasar UAE ta yi murabus daga aikinta saboda kasar ta kulla alaka da Isra’ila.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na skywaterjo ya bayar da rahoton cewa, Rana Ibrahim Katibah, daya daga cikin jami’an ‘yan sanda na birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa


wadda asalinta bafalastiniya ce ta yi murabus daga aikinta saboda kasar ta kulla alaka da gwamnatin yahudawa.


A cikin takardar da ta rubuta wa babban kwamishinan ‘yan sanda na birin Dubai, Rana ta bayyana cewa a matsayinta na balaraba musulma mai kishin addininta da kabilarta, ba za ta taba yin aiki da duk wata da ta kulla alaka da kawance da haramtacciyar kasar Isra’ila ba, wadda ta mamaye musu kasa bisa zalunci.


A kan haka ta ce ta yi murabus daga aikinta a matsayinta na ‘yar sanda a kasar hadaddiyar daular larabawa, saboda wannan kasa ta mika kai wajen kulla alaka da yahudawa wanda hakan ita ya sabawa imaninta da akidarta.


Ta kara da cewa hatta shedar zama dan kasa da aka bata a UAE ba ta da bukata, kuma bata da bukatar kudin sallama daga aiki, ta ce ta bayar da wadannan kudin kyauta ga cibiyoyin da suke gudanar da ayyukan taimako ga mabukata.

SOURCE: ABNA24.COM

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post