Jiya naje gidan mai akan babur dina domin sayen mai, na mika kudina dari biyar nace a bani mai na dari hudu, ban ankara ba, kafin ayi haka! Sai naga har an gama zubamin mai, na tambayi zuciyata wai har an zubamin man dari hudun?
Sai na kalli litar mai naga man da nasha, sai naga lita 2.6 na sake duba wajan da ake rubuta farashin kudin mai, banyi aune ba sai naga ansa farshi naira dari da hamsin Lt-150. Abin ya dauremin kai na tambayi masu gidan mai wai yaushe aka kara kudin mai yazama naira dari da hamsin, sai sukace ai an kai kwana uku.
Da farko nayi niyyar inyi bambami akan rashin tausayinsu na ganin tsohon mai garesu amma daga kara kudi har sun kara. Wanda idan da ragine akayi bazasu rageba.
Nan take sai nasake tunani cewa ai ba sune masu laifi ba, gwamnati ce ta kara, sai nayi sakwat nayi jangwam, nace oh! Ni Musa! Talakka nashan shegiyar wuya a hannun gwamnatin buhari wadda yayita fafutukar ganin ta kafu da tunanin samun sauki.
In waiga haka sai naga wani abokin gwagwarmaya shima an tsiyayamasa na naira dubu a motarsa yana kokwanto wai na dubun kuwa aka zuba. Nace masa na dubune ai baifi lita shidda ba. Nan take muka koma gefe guda muna guna guni, muna al'ajabi akan wannan lamari na gwamnatin Buhari.
Daga karshe muka tabbatar dacewa gaskiya gwamnatin Buhari ta bayar da mutanen kasar nan musamman talakka, ganin yadda kullum azaba ke karuwa, ta safe da ban, ta yamma da ban haka kuma ta dare da ban. DAGA NAN NA FARA TUNANIN SHIN WAI ANYA KUWA BUHARIN DANA SANI NE MAI CEWA YANASON TALAKKA YAJI DADI KE MULKIN MU, KO KUWA GASKIYAR NMANDI KANU, JIBIRIL AS-SUDAN NE KE MULKIN NAJERIYA?
Idan kuwa har Buhari ne wanda mukewa kirari da dogo Dan Daura jagoran talakkawa to a gaskiya BUHARI, yakamata ka sake nazarin yadda ake tafiyar da kasar nan kayi bincike kaji yadda talakka keshan shegiyar wuya shekara shidda tun shigowar gwamnatin ka, wallahi talakkawa sun yanke kaunar samun saukin rayuwa a mulkin ka, duk da dai ba'a yanke kauna daga rahamar Allah.
Shugaba buhari wallahi talakka na kuka babu sauki ta kowace hanya, tsaro ya tabarbare a wasu sassan kasar nan, tattalin arziki yayi rugu-rugu mutane duk sun karye wasu bashi ya danne su, kuma bazasu sake tashi ba, harkar noma babu taki, sai ansa kudi masu yawa a saya, abinci yayi masifar tashi, babubkudin sayen magani, cin hanci yayi katutu anaji ana gani wasu sun azurta kansu da kudin kasa kuma duk a mulkin mai gaskiya da rikon amana, anya kuwa?
Daga karshen, karshe ina fatan shugaba buhari bazai bari yayi fargar JAJI BA, WANDA YA TAFI YAKI SAI DA AKA FILLE MASA KAI SAI YA TUNA DA LAYAR ZANARSA, YA DAFATA, SAI GA KAI A KASA GANGAR JIKI TA BACE.
Sai kun sake jina, tunda na samu yau na dan leko ku da kyar!
MUSA IBRAHIM DAURA
09-8-2020.
Tags:
Daga marubata