Waye Sheikh Abduljabbar? Assheikh Abduljabbar Ibn Sheikh Nasiru Kabara malamin Addini ne,kuma ɗan ɗarikar ƙadiriyyah ne shi mai bin mazhabar Imam Malik. San'nan kuma har yau Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru kabara baitaɓa Ayyana kansa ba a matsayin ɗan shi'a. Amma yabada gudumawar da irin Ustazu Hamza Lawal ɗari (idan akwaisu) basu bada ba.
Domin a tarihin Hamza Lawal bai taɓa ɗauko wani mutum daga gidan Sunnah ba, idan nace gidan sunnah ina nufi Hamza bai taɓa ɗauko wani bawahabiye ko sufi, ya maida su 'yan shi'a ba. Ko ta hanyar wa'azin sa ko ta hanyar mu'a malar sa ko kuma ta hanyar kyakykyawar ɗabi'ar sa. (Idan yana da ita)
Mutanen da Hamza Lawal ke tare dasu, dukkansu za'a iya cewa 'yan harkar musulinci ne, waɗanda ko wace irin tafiya zaka samu mutane iri uku ne, akwai waɗanda zakasamu suna yin harkar ne domin neman tsira ga Allah (s.w.t) ko nace kyakykyawar makoma, to 'yan tsirarun waɗanda Hamza Lawal ya ɗiba za'aga wasu irin mutane ne da suka cika da son rai dakuma son duniya gami da tunanin tayaya zasu iya bunƙasa kansu.
To shikuma tunda yana da Usulubi na kada a gyaru, ma'ana Al'uma su dunga tafiya bisa wani tsari wanda kai tsaye yake yaƙi ko fito na fito da tsarin Allah subhanahu wata'ala to shi yajaza suka bishi, inma dai da ra'ayin siyasa kokuma goyama Azzaluman shiwagabanni baya, wan'nan kuma yarigaya ya zama wani abu wanda yake sananne akan shi Hamza ɗin.
San'nan kuma shi Hamza lawal baki ɗaya rayuwar sa, yayi karatu ne a wajen malaman Shi'a na tsawon shekara uku ko ƙasa ga haka, wanda a Nigeria akwai malaman da suka shekara ashirin wasu ashirin da biyar wasu ma talatin a gaban malaman shi'a, wasu a Iraq wasu a Iran wasu a Lebonan. Amma basu ɗauki irin Usulubin Hamza ba na cin mutunci da raina magabata.
Hamza lawal bashi da wani tarihi ko shi ko gidansu,babu wani tarihi sajjalalle na ilimi, amma Sheikh Abduljabbar Nasiru kabara a rayuwar sa da yayi ta shekara hamsin ya rubuta littafi ɗari, wanda aƙalla guda hamsin daga cikin su sun fito hannun al'uma suna yawo.
Iya Abinda muka fahimta da Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru kabara a matsayin sa na shi ba ɗan shi'a bane amma malami ne da yake da wula'a da Ahlulbayt (a.s) wanda kuma a ra'ayin Sheikh Abduljabbar babu wani mutum da yake tare da manzon Allah wanda za'a fifitashi akan jinin Manzon Allah(s.a.w.w) kacokaf sahabban Manzon Allah (s.a.w.w) babu irin Ali ibn Ɗalib kuma wan'nan shine dama ra'ayi sufaye baki ɗaya.
A kullum aikin Sheikh Abduljabbar shine tayaya za'ai a ruguza wata aƙida ko koyarwa wadda take taɓa janibin Manzon Allah(s.a.w.w) arusa duk wanda yazo da wan'nan koyarwar, wan'nan shine aikin sa.
Aikin Hamza lawal: ƙarya ƙazafi cin mutunci ƙoƙarin yaga ta yaya zayayi domin ya burge mutane, duk'wanda ya saɓamasa jahili ne, duk wanda suka saɓa a fahimta jahili ne, idan yana magana a gaban mutane ƙwaƙwalwar sa tafi ta kowa, yafi kowa hangen nesa, yafi kowa ganewa, yafi kowa iyawa, bai yarda ba ace akwai wani mutum daga mahudar rana zuwa mafaɗar ta wanda ya fishi ba. Babu wata sifa da zaka bawa Hamza lawal inbaicin kakirashi mahaukaci wanda ya samu matsala ta tunani da ƙwaƙwalwa.
Agaskiyar lamari inada ra'ayin Sheikh Abduljabbar kada ya biyema ruɗaɗɗu, kada kuma ya biyema wan'nan mutimin da yake so sai ya tallata kansa.
Kobakomi Hamza lawal yayi faɗa da 'ya'yan harka Islamiyya domin neman suna, sabida lokacin da ya fara faɗa da malam (H) malam baya nan, sai yasamu matsala har yau babu wani mutum fitacce a harka da yabiye masa, sai aka barshi da yara kanana. Saboda haka tunda yaga a harka haryanzu baiyi sunan ba, acikin Badikko ma ba'a sanshi ba-ballanta na kaduna, Anshiga rediyo FM anshiga talabijin anshiga rediyon tarayya kaduna, duk inda ake shiga a nemi suna anshiga, anyi kankanbar yaren turanci,anyi kankanbar ƙalƙala, anyi kankanbar ƙa'ida.
Ya bayyana kansa a matsayin malamin bariki cikakke, amma dai hajar taƙi kasuwa mutane sunki saye, to Allah shi kyauta.
Amma dai Sheikh Abduljabbar mu muna tare dashi ɗari bisa ɗari akan ɗaga tuta ta Ahlulbayt (A.S) irin Hamza dubu ba zasuyi Abduljabbar ɗaya ba.
Da murasa Sheikh Abduljabbar a ƙasar nan Gwamma mu rasa Duka Hamzojin ƙasar nan idan har akwai irin su, saboda gaskiya irin waɗan'nan Hamzojin kansa ne acikin Addinn musulinci, kuma muna fata Allah yayi mana maganin sa.
NURA BISHIR KT.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Muhimman zantuka