ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya ce majiyar ta kara da cewa fiye da motocin yaki na kasar Turkiya 5,000 ne suke cikin lardin Idlib a halin yanzu.
Labarin ya kara da cewa halin yanzu gwamnatin kasar Turkiyya ta na da sojoji kimani dubu 11,500 a arewacin kasar ta Siriya.
Gwamnatin kasar Turkiyya dai ta shigo kasar ta Siriya ne da sunan yaki da ‘yan ta’adda tun shekara ta 2011, amma a halin yanzu tana mamaye da wasu yankuna a arewacin kasar ta Siriya, sannan a wasu lokuta sojojin kasar sukan budewa juna wuta da sojojin kasar Siriya.
SOURCE: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com