`Ma'asuma Nigeria news update`
Daga makarantar Ahlulbyt {As},
Imami na biyar na makarantar Ahlul-bayt (Imam Muhammad al-Baqir) ya taba fada wa dalibinsa (Jabir) wanda ya tambaye shi cewa : Shin ya isa ga mutum ya ɗauka ko bincika kansa a matsayin mabiyan ku ta hanyar nuna muku ƙauna {Ahlulbyt},
Imam ya amsa, mutum ba mai bin mu bane sai dai in ya ji tsoron Allah ya yi masa biyayya.
Ya Jabir! Mabiyanmu ne kawai ake gane su da tawali'u, biyayya, gaskiya, yawan yabon Allah, azumi, addu'o'i, kyautatawa iyayensu, mai da hankali ga matalauta / mabukaci / kula da marayu da ke rayuwa a kusa, suna faɗin gaskiya, karatun Kur'ani, kamewa da harshensu basa furta komi sai kyawawan kalmomi, da rikon amana ga dangin dangi a cikin dukkan al'amuran su.
(Al-Kulayni al-kafi Mujalladi 2 Shafi 74) .
An sadaukar da wannan post din ga, Shaheed Aliyu Ibrahim Galadanci,
Tunda ‘yan Shi’a mabiyan Ali ne, to, wanene Wannan Ali kenan?
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Taskar ilimi