Bayan Imam Husaini Ya Karya Siddi Ya Nufi Kufa Domin Baisan Abun Daya Faru Da Muslim Da Hani'u Ba, Sai Abdullahi Bin Jafaru Addayalisiy da Yayansa Suka Rubutawa Imam Husaini Takarda Suna Mai Cewa Karka Tafi Kufa Kasan A Kufa Aka Kashe Babanka Ali As Aka Kashe Dan Uwanka Hassan As , idan Ka Kwashi Zuriyarka Ka Tafi Wallahi Ka Tunbike Albarka A Ban Kasa Saboda Duk Za'a Kashe Su Kuma idan aka Kashe Su Kasa Ta Koma Duhu Kar Ka Tafi Zanzo Idan Ka Samu Takardata ka jirani
Haka Na Amratu Yar Abdurrahan Ansariyyah Itama Tana Madina Ta Aiko Tata Takardar Tana Cewa Kar Ka Tafi Domin Naji Aisha R.a Tana Cewa Taji Annabi Saw Yana Cewa Za'a Kashe Husain A Babila (Karbala) Inka Fita Wannan Hadisin Zai Tabbata , Da Aka Kawo Masa Takardar Ya Duba Sai Yace Ya Zama Dole Kenan Na Naje Inda Za'a Kwantar Dani .
Abdullahi Bin Umar Shima Yayo Siddi Yazo Ya Sami Alhusaini Yace Karka Fita Ya Rungume Shi Imam Husain Yace Tayaya Zan Hakura Da Fita Inda Allah Ya Zabarmin , Idan Ni Nai Nasara Dasu Haka Allah Yaso Idan Su Sukai Nasara Dani Haka Allah Ya Tsara , Abdullahi Yace Ina Bankwana Da Kashasshe , Alhusaini Yace Ya Abdullahi Bakasan Saboda Wulaqantar Duniya Ba Akai Kyautar Kan Annabi Yahya Aka Baiwa Karuwa Shi !
Na Rantse Da Allah Dazan Shiga Wani Kwazazzabo A Makka Na Buya Sai Sun Zo Sun Biya Bukatar Su Akaina , Zasuyi Ta'addaci Akaina Kamar Da Yahudu Sukai Ranar Asabar , Ya Abdullahi Na Fita Naje Su Kashe Ni A Karbala Ko Babila Ko Shaddil Firati Shi Yafimin A Guna Dana Zauna Su Kashe Ni A Cikin Makka Su Halatta Alfarmar Makka Dani ! !
Imam Hussain Ya Karya Lunzami Ya Fita Yana Mai Karanta Ayar Allah - LI MALIN WA LAMAKUM AMALUKUM ANTUM BARI'UNA MIMMA A'AMALU WA ANTUN BARI'UNA MIMMA TA'AMALUN
Yayin Da Labari Yajewa Yazedu Cewa Ga Alhusaini Ya Nufi Kufa Sai Ya Aikawa Ubaidullahi Wasika Yana Cewa - Labari Ya Iso Min Cewa Husaini Ya Nufi Karsar Ka , To Ka Sani , Allah Ya Jarrabaka Da Husaini Ya Jarrabi Zamaninka A Cikin Zamaninnika, Bai Duba Wani Zamani Da Zai Hijra Ba Sai Da Muka Tura Ka , To Muna Sa Ido , A Yanzu Ne Zaka Zama Da Ko Ka koma Bawa -Wassalam
Yayin Da Alhusaini Yaje Wani Kauye Da Ake CE Dashi Sa'alabiya Anan Ya Samu Labari An Kashe Muslim Bin Aqil Da Hani'u Bin Urwa , Ta Hanyar Wani Daga Cikin Mayaqan Yazedu Yace Aje A Fada Masa Karya Karaso An Kashe Muslim Da Hani'u , Imam Husaini Yaita Istinja'i Yana Neman Musu Gafara Idanuwansa Ya Zub Da Hawaye
Ya Fito Yana Fadawa Jama'ar Sa Abunda Ya Faru Yana Mai Cewa -Jama'ar Mu Sun Tozartamu ,Dan Haka Duk Wanda Yake So Ya Koma Gida To Ya Koma Shida Iyalansa Na Yarje Masa , Nan Fa Jama'a Suka Watse Daga Shi sai Yan Tsirari , Wannan Baisa Ya Kunce Damararsa Ba Sai Ya Kuma Daura Siddi Yai Gaba . Sai Da Yaje Wani Qauye Da Ake Ce Masa Shiraf Anan Ne Suka Sake Shiri Aka Debi Ruwa Aka Baiwa Dabbobi Kowa Yai Guziri ,
Suna Tafiya Da Mil Biyu Sai Suka Ga Dawaki Iya Ganinsu Sunyi Musu Qawanya Kimanin Mahaya Dubu Da Na Kasa Dubu , Imam Husain Yasa Aka Kira Sallah Akai Sallah Bayan An Idar Imam Husain Ya Tafi Yace Yaku Jama'a Ta Ku Sani Idan Kunji Tsoran Allah Kuka Bi Gaskiya Kukai Aiki da Abun Da Zai Yardar Da Allah , Mune Aula Daku Dafawa Basu Yazedu Ba , Da'awa Suke Da Muqamin Da Ba Nasu Ba , Suna Mulki Da Zalunci Da Ta'addanci , Amma Inkunce Bakwa Sonmu Kuka Jahilci Ko Suwaye Mu Kuka Karya Alkawarin Da Kuka Rubuton Da Ina Makka To Sai Na Koma
Anan Hurru Bin Yazidar Yarbu'iy Yace Mu Bamu Yi Maka Wata Takarda Ba , Alhusaini Yace Da Uqubatu Bin Sam'ana Ya Dauko Kurtajin Da Ake Aje Takardu Aka Dauko Saiga Takardu Hamsin 50 Nan Duk Da Tambari , Sai Hurru Yace Nifa Abun Da Aka Turo Ni Kawai Naxo Na Tare Ka imam Husaini Yace To Shikenan Zan Tafi Babu Aibi Ga Mutuwa Domin Da Da Aibi Da Annabawa Basu Mutuba Dan Haka Kune Akan Aibi ba Niba .
Jawad Salisu Attaqiy Alganawiy